Hedikwatar Hukumar tsaron ƙasa DHQ ta bayyana cewa babban kwamandan ‘yan bindiga Saleh Mustapha ya mika wuya ga rundunar ‘Operation Hadin Kai’ a Arewa maso Yammacin kasar nan.
Hukumar ta Kuma ce akalla ‘yan ta’ada 51,114 ne suka mika wuyan ga dakarun sojin Najeriya.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka ranar Alhamis a Abuja da yake bayyana aiyukan da dakarun sojin Najeriya suka yi daga ranar 25 ga Maris zuwa 7 ga Afrilu.
Onyeuko ya ce mika wuyan da Mustapha wanda aka fi sani da Inn Kathir kuma kwamandan ‘yan bindigan dake Garin Ba-Abba nasara ce babba ga sojoji a Bama.
Ya ce daga cikin ‘yan ta’adda 51,114 da suka mika wuya ranar 5 ga Afrilu akwai maza 11,398, mata 15,381 da yara 24,335 wanda aka damka wa jami’an tsaron da ya kamata domin ci gaba da gudanar bincike.
Daga nan Onyeuko ya ce makonni biyu da suka gabata dakarun sojoji sun kama motar yaki guda daya bindigogi biyar kirar Artillery guns, bindigogi biyu kiran GTS da bindigogi uku kisan AA.
Sauran makaman da dakarun suka kama sun hada da mota kiran MRAP, motar bindiga guda uku, mota kiran MOWAG guda daya da RPG guda biyu.
Akwai kuma nakiyoyi kirar RPG guda uku, RPG guda uku, bindiga kirar NSVT guda daya, GPMG biyu, MaG daya, PKM daya jigidar harsashin bindiga guda uku da jigidan PKT guda hudu.
Ya ce dakarun sun kuma kama harsashin bindiga kirar NATO guda 600, harsashin bindiga kirar AK 47 guda 16, mota kirar Toyota Buffalo guda daya, mota kirar Golf saloon guda daya, babura hudu, fankon harsashi shida, kayan sojoji biyu, Keke NAPEP daya da na’uran drone daya.
Bayan haka Onyeuko ya ce dakarun sun kashe ‘yan ta’ada da dama sannan sun kama ‘yan leken asirin ‘yan ta’adda 22, sun kama wasu ‘yan ta’adda 11.
Rundunar sojin Sama ta babbake rumbun makaman ‘yan ta’addan ISWAP dake maboyar su dake Bukar Meiram da Kollaram tsakanin ranar 28 zuwa 32 ga Maris.
Rundunar sojin sama tare da hadinguiwar na ƙasa sun kai wa sansanin maharan dake Ukuba/Camp Zairo, Sabil Huda, Ba Masaa, Wulgo, Marta, kauyen Fulatari, Uraha, Mbalala, garin Gamboru duk a jihar Borno.