Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Tarayya, Muktar Betara (APC, Barno), ya bayyana cewa kasafin harkokin tsaro na fuskantar ƙarancin kuɗi ne saboda maƙudan kuɗaɗen da ake warewa na tafiya ne wajen biyan albashi da ayyukan yau da kullum, maimakon wajen gudanar da manyan ayyuka.
Betara ya ce wannan irin kason kasafin kuɗi na shafar jajircewar ayyukan jami’an sojoji wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga.
Ya bayyana haka ne a lokaci da ya ke zantawa da manema labarai dangane da batun gyaran Dokar Kasafin Kuɗi ta 2022.
Ya ce aƙalla majalisa ta amince a biya ‘yan sanda albashin Naira biliyan 182.
A ranar Alhamis ɗin nan ce Kwamitin Lura da Sauran Kayayyaki ya amince da rahoton Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe kan kwaskwarimar dokar kasafin, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya nema su amince ɗin. A ciki kuwa har da batun biyan ‘yan sanda albashin Naira biliyan 50.
Betara ya ce matsalar sojoji ta ƙarancin kuɗaɗen biyan manyan ayyuka ce da kuma ayyukan yau da kullum da ba su da su a wadace cikin kasafin kuɗaɗe.
Ya ce albashin Sojojin Najeriya kaɗai na lashe Naira biliyan 400, alhali kuma adadin kuɗaɗen kasafin manyan ayyuka ba su wuce Naira biliyan 30 ba.
Ya ce ƙarin da aka yi wa ‘yan sanda kuma ya ce duk a wajen biyan albashi za a kashe su.
“Mu na cewa ana danƙara wa Hukumar Sojoji kuɗaɗe, amma wai ba su yin komai ko kuma ba su yin abin da ya dace su yi da kuɗin. To ku sani albashi ke cinye kashi 80 bisa 100 na kasafin kuɗin Sojojin Najeriya. Kuɗaɗen ayyukan yau da kullum ba su ma wuce Naira biliyan 20 da ɗan wani abu ba. Kasafin manyan ayyukan sojoji kuma Naira biliyan 37.
“Don haka idan ku ka kalli kasafin kuɗaɗen, za ku ga duk holoƙo ne, hadarin kaka.”