Gwamnan jihar Ribas Nysome Wike ya bayyana wa ƴaƴan jam’iyyar PDP a jihar Edo cewa bai fito takara don a yi masa mataimakin shugaban kasa bane, ya fito don zama shugaban kasa ne.
” Ni fa ba mataimakin shugaban kasa na fito nema ba, kujerar da Buhari yake, wato ta shugaban kasa ita na fito biɗa. Saboda haka a shirye nake kuma dani za a fafata. Ina son kowa ya san haka.
Wike ya kara da cewa babbbar matsalar da ya sa natsalar rashin tsaro yaki ci yaki cincewa a kasar nan shine na rashin gwamnati ta kashe makudan kuɗi a hanyar samar da bayanan sirri game da tsaron kasa.
” Dole sai an ware makudan kuɗi an kashe su a harkar zaƙulo bayanan sirri a Najeriya domin ganawa da ƴan bindigi da matsalar rashin tsaro in ba haka ba kuwa za a yi ta fama ne, jiya iyau.
” Ni bana cika baki, a je a duba ayyukan da na yi. Su kaɗai sun ishe ni bugun ƙirji da su, in yi nasara a zaɓe.
” Idan PDP na son su dawo kan mulki a Najeriya, nine shafaffe da man da zai iya yin wujiwuji da APC a zabe mai zuwa, PDP ta tabbata ta tsaida ni takara kawai.
A karshe Wike ya ce tabbas Najeriya na bukatar shugaba wanda ya kware, sannan ya jajirce wajen sanin makaman aiki da hayagagar siyasa, da kuma samin yadda za a shawo kan matsalolin kasa. ” Ni ne kuma gogarman da ya goge a wannan harka saboda haka kowa ya shirya kaɗa masa kuri’a idan lokacin zabe ya yi.
Discussion about this post