Babban ɗan tsohon fitaccen ɗan siyasa, Moshood Abiola, Kola Abiola ya tsinduma siyasa, ya shiga jam’iyyar PRP.
Da yake yi masa wankan shiga jam’iyyar PRP, shugaban jam’iyyar Falalu Bello ya ce jam’iyyar yi wa Kola Abiola maraba da shiga PRP.
A jawabin da yayi a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja Abiola ya ce ya shiga PRP ce saboda akidar jam’iyyar na komai don talaka.
” Na shiga jam’iyyar PRP ne domin in nuna wa ƴan Najeriya cewa lallai akwai lokacin da akayi abubu a kasar nan kuma aka yi nasara, kasa ta ɗau saiti komai na tafiya yadda ya kamata. Kafin ƴan siyasan yanzu su zo su daburta komai.
” Ni mutum mai son a baiwa kowa dama daidai yadda yakamata babu nuna banbanci, wariya ko karfin iko.
” Abu ɗaya da zan fi maida hankali a kai shine in kawo karshen siyasar ubangida a kasar nan, kuma matasa su san da haka.
” Akalla kashi 75 cikin 100 na ƴan Najeriya yanzu, matasa ne, dole a basu wuri domin damawa da su a fagen siyasa a kasar nan wanda shine buri na kuma abinda zan fi maida a hankalai a kai kenan.
Idan ba a manta ba mahaifin Kola Abiola, wato MKO Abiola shine ake kyautata zaton ya lashe zaben shugaban kasa a 1991 wanda gwamnatin Ibrahim Babangida ta soke.
MKO Abiola ya rasu a lokacin mulkin marigayi Sani Abacha.