Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya bayin Allah! Babban Malamin mu, Ash-Sheikh Sulaiman Ar-Ruhaili yana cewa:
“Yaku masoyana ina yi maku kashedi game da Allah, ku kiyayi Allah, hakika Allah yayi maku ni’imah, kasancewar ya sanya ku cikin wadanda suka riski wannan wata na Sha’aban, alhali kuna cikin koshin lafiya da karfi da alkhairi. Don haka, ku godewa Allah mai girma da daukaka a bisa wannan ni’imar da yayi maku; ku kyautatawa kanku ta hanyar yawaita azumi a wannan wata na Sha’aban, la’alla Allah ya sanya ku cikin wadanda zasu samu Aljannah, a dalilin azumtar wannan wata da kuka yi, kuma ya ‘ƴantar da ku daga azabar wuta. Yaku bayin Allah! Ina yi maku gargadi da kashedi, game da Allah, a bisa wannan ganimar da ya baku. Kada kuyi sakaci da ita, kada kuyi kasala a cikinta. Kuyi rige-rige a cikinta, wurin aikata ayukkan alkhairi. Ku sani, abun sayarwar yana da tsada, hakika abun sayarwar Allah shine Aljannah. Kuma tabbas, kudin sayenta da ake nema a wurin ku, dan kadan ne, ya ku bayin Allah.”
Ya ku masoyana, masu girma! Imam Abubakar Al-Bulkhi Allah yayi masa rahama, ya kasance yana cewa:
“Ku sani, watan Rajab wata ne na shuka, watan Sha’aban kuma wata ne na ban ruwa (wato bayi), watan Ramadan kuma wata ne na girbi.”
Sannan ya kara da cewa:
“Watan Rajab kamar iska ne (wato guguwa), shi kuma watan Sha’aban kamar hadari ne, shi kuma watan Ramadan shine ruwan saman.”
Wani babban Malami daga cikin magabata yana cewa:
“Shekara tana nan kamar bishiya ce, watan Rajab shine lokacin fidda furen ta, watan Sha’aban kuma shine lokacin fidda ‘ya’yanta, watan Ramadan kuma shine lokacin tsinkar ‘ya’yan, kuma muminai sune suka cancanci tsinkan ‘ya’yan. Ga mutumin da ya bakanta littafinsa da zunubai, sai ya faranta shi da tuba zuwa ga Allah a cikin wannan watan, wanda kuma ya bata shekarunsa a banza, to sai ya ribaci abunda ya rage na shekarunsa.”
Uwar Muminai, Ummu na Aisha Allah ya kara yarda da ita, ta ke cewa:
“Manzon Allah ya kasance yana yin azumi a cikin wannan watan, har sai munyi tsammanin ba zai ajiye ba. Sannan idan ya ajiye, har sai munyi tsammanin ba zai dauka ba.”
Sannan ta kara da cewa:
“Ban taba ganin Manzon Allah (SAW) ya azumci wani wata gaba ɗayan sa ba, sai Ramadan. Sannan babu wani wata da Annabi yake yawaita azumi a cikinsa kamar Sha’aban.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito]
Habib Bin Thabit Allah yayi masa rahamah, ya kasance idan watan Sha’aban ya kama, yana cewa:
“Wannan (watan Sha’aban) shine watan Kurra’u (wato watan makaranta Alkur’ani).”
Amru Bin Kais Al-Mula’i Allah yayi masa rahamah, ya kasance idan watan Sha’aban ya kama, yana kulle shagonsa, ya kebance kansa ga karatun Alkur’ani kawai.
Salmata Bin Kuhail, Allah yayi masa rahamah, yana cewa:
“Ya kasance ana kiran watan Sha’aban da watan Kurra’u.”
Alhassan Bin Shahil, Allah yayi masa rahamah, ya kasance yana yawaita karatun Alkur’ani a cikinsu (wato watan Sha’aban da watan Ramadan) sannan sai yace: “Ya Allah, ka sanya ni a tsakanin watanni guda biyu masu girma.” [Duba littafin, Lata’iful-Ma’arif]
Usamah Bin Zaid yace:
“Ya Manzon Allah, ban ga kana azumtar wani wata kamar yadda kake azumtar Sha’aban ba? Sai Annabi (SAW) yace: Wannan shine watan da mutane suke gafala da shi, tsakanin Rajab da Ramadan, alhali wata ne da ake kai aikin bayi zuwa ga Ubangijin Talikai, shine nike son akai aiki na wurin Allah alhali ina cikin azumi.” [Nasa’i ne ya ruwaito shi, kuma Sheikh Albani ya inganta shi]
An ruwaito daga babban Sahabi, Anas Bin Malik, Allah ya kara yarda da shi yace:
“Sahabban Manzon (SAW), sun kasance idan watan Sha’aban ya kama, sun dukufa kenan akan Alkur’ani, suna karanta shi, sannan su fitar da zakkar dukiyarsu, su karfafi masu rauni, da miskinai, da marasa galihu, a kan azumin watan Ramadan, sannan Musulmai su kira bayinsu, su ce mun yafe maku harajin da ke kanku a cikin watan Ramadan (Abun nufi, wato sun yafe masu. Babu biyan haraji a kansu, har Ramadan ya wuce). Shugabanni kuma su kira ‘yan fursuna, wanda yake da hukuncin haddi sai ayi masa. Wanda kuma laifinsa babu haddi sai a yafe masa, a sake shi ya tafi. Sannan kuma shugabannin al’ummah suna raba kayan arziki ga talakawa” [Duba littafin IKHRAJI-ZAKAT na Ibn Rajab Al-Hanbali]
Ya ku bayin Allah masu girma! Mu dage da addu’a a wannan lokaci mai albarka, musamman a kan matsalolin da suke addabar wannan kasa tamu mai albarka, da kuma yankin mu na arewa. Ku sani, ita addu’a ba ta faduwa kasa banza!
Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace:
“Babu wani Musulmi da za ya roƙi Allah da wata Addu’a wadda babu sabon Allah a cikinta ko kuma yanke zumunta, face sai an bashi ɗayan abubuwa uku: ko dai Allah ya gaggauta bashi abinda ya roƙa nan take, ko kuma Allah ya jinkirta masa sai a lahira a biya shi, ko kuma ya kawar masa da wani mummunan abu da zai same shi. Sai Sahabbai suka ce, lallai zamu yawaita yin addu’a kuwa. Sai Manzon Allah (SAW) yace, Allah zai yawaita.” [Imam Ahmad ne ya ruwaito]
A dage da addu’a ya bayin Allah, sannan a guji yin gaggawa wurin amsawa!
Sannan ‘yan uwana Musulmi, duk yadda za’ayi, kada ku bar zikirorin safiya da kuma na marece, domin zasu kusanta ku ga Allah. Sannan zaku samu kariya daga dukkan abin ƙi, na daga shaidanu da mutane. Kuma kariya ne daga sharrin hassada, da kambun baka, kai da ma dukkan wani abu mai cutarwa!
Ya Allah, ka nuna muna Ramadan muna masu Imani da koshin lafiya.
Ya Allah, kasa muna daga cikin bayin ka da zaka ‘ƴanta a cikin wannan wata mai albarka.
Daga karshe, Abu Darda yana cewa:
“Babban abun tsoro na shine, in tsaya a gaban Allah ranar sakamako, ace da ni, Abu Darda, me kayi da ilimin da ka koya?” [Duba littafin Addaʾu wad-dawa’]
Dan uwa na mai daraja, abun tambaya a nan shine: Shin da ni, da kai, da ke, da ku, da su, mun taba tambayar kawunan mu game da yadda muke sarrafa abunda muka koya na ilimi kuwa? Shin mu ma wane tanadi mu kayi wurin amsa wannan tambayar a gaban Allah, gobe kiyama?!
Sannan a kashe, wallahi ina shaida maku cewa, duk wanda yake son ya more wa rayuwar duniya da ta lahira, to yabi Allah…!
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, jihar Kogi, Najeriya. Za’a same shi a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post