Kotun majistare dake Iyaganku a Ibadan jihar Oyo ta yanke wa Auwal Salisu hukuncin zama a kurkukun dake Abolongo.
Ƴan sanda sun gurfanar da Salisu bayan an kama shi da laifin kashe wani manomi dan kasan Togo Kosi Apaji a kauyen Aada ranar 17 ga Janairu.
Dan sandan da ya shigar da kara Femi Oluwadare ya ce a wannan rana Salisu ya fille kan manomin sannan ya daddatse kafafun sa a lokacin da yake aiki a gonar sa.
Oluwadare ya ce hakan da Salisu ya yi ya saba wa dokan ‘Criminal code’ ta shekaran 2000 na jihar Oyo.
Alkalin kotun Emmanuel Idowu ya yi watsi da rokon sassauci da Salisu ya roka.
Idowu ya ce Salisu zai yi zaman kurkuku har sai kotun ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifukq irin haka ta jihar.
Za a ci gaba da shari’a ranar 4 ga Afrilu.