An nan ana ta shirye shiryen ɗaurin auren Sarkin Iwo Adewale Akanbi (Telu 1) da Firdauz Abdullahi jikan sarkin Kano marigayi Ado Bayero wanda ɗiya ce ga sarki Aminun Kanawa.
Tun bayan rabuwar sa da matarsa diyar shahararren mawakin Rege Ludlow Chin bai sake aure ba. Sun rabu suna da ɗa ɗaya tare da Chanel Chin, wanda ya saka wa suna Oduduwa.
Bayanai da suka fito daga fadar sarkin Kano game da auren sun nuna cewa za a ɗaura auren a gidan madakin Kano ranar 19 ga watan Maris.
Bayan haka mata za su dunguma zuwa wurin liyafar cin abinci wanda aka shirya wa mata a gidan Rumfa dake fadar mai martaba sarki.