Kwamishinan Ƙananan Hukumomin jihar Kano Murtala Sule Garo ya bayyana wa BBC Hausa cewa shi ya kai kansa ofishin hukumar SSS domin amsa gayyatar da hukuma da yi masa da wasu ba hannun daman gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje.
Hukumar ta gayyace su ne domin amsa tambayoyi game da matsalolin rashin tsaro da ake samu da suka danganci siyasa.
Garo ya tabbatar wa BBC cewa yana cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka mika kansu ga DSS domin amsa gayyatar da humar ta yi musu.
Sauran gaggan ƴan siyasan kuma na gaban goshi. gwamna Ganduje sun hada da Fa’izu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Birnin Kano; Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale; da Injiniya Bashir Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo.
Garo ya ce hakazalika an gayyaci ɗan takarar gwamnan jihar A.A Zaura; da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa; da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi, da kuma wani mai bai wa Gwamna shawara.
DABANCIN SIYASA A KANO
Magoya bayan kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano Murtala Sule Garo da na Kabiru Rurum sun kaure da fada a wajen kaddamar da sabbin shugabannin APC da aka yi a filin Taro na Rano a karshen makon jiya.
Rikici ya barke ne a lokacin da magohya bayan jigajigan ‘yan siyasa a lokacin da suka hadu a wajen taron.
Baya ga mutum hudu da aka kashe anji wa mutane da yawa rauni a wannan arangama.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya raba motoci ga ‘yan siyasa da bayan rantsar da shugabannin jam’iyyar a garin Rano.
Dan uwan daya daga cikin wanda aka kashe Abba Abdullahi, Hamisu Abdullahi da aka fi kira da AGA, wanda kuma mahauci ne ya ce a wannan rana dan wuansa ya ki zuwa kasuwa aikin nama ya nausa can wurin taro inda a nan ne aka kashe shi.
Abba ya ce an yi wa Aga mummunar sara ne a wuya ashe kuma ya zo da karewar kwana. Ya rasu ya bar matarsa daya da ‘yar sa daya.
Haka shima, Dan-Mamadu Kaura daga Garo ya rasa ran sa a wannan rikici. Ya rasu a wani asibitia cikin Kano.
Bayan su akwai wasu mutum biyu da suka rasu a sanadiyyar rikicin a wannan wurin taro.