Kwamishinan Kasafin kuɗin jihar Kaduna, Mohammed Abdullahi, wanda aka fi sani da Dattijo ya kaddamar da kamfen ɗin takarar gwamnan jihar Kaduna ranar Talata.
Mohammed Abdullahi Dattijo ya bayyana wa manema labarai cewa ya fito takara ne domin a cigaba da ayyukan da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yake yi a jihar.
Idan ba a manta ba, Mohammed Abdullahi na daga cikin ƴan gaban goshin gwamna Nasir El-Rufai wanda ake ji da su a mulki.
Ya fara zama kwamishinan kasafin Kuɗi a 2015 zuwa 2019.
Bayan jam’iyyar ta dawo kan karagar mulki a 2019, sai gwamna El-Rufai ya nada shi shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.
A cikin shekarar 2021 kuma sai aka sake naɗashi Kwamishinan kasafin Kuɗi na jihar, mukamin da yake kai har yanzu.
Dattijo ya ce ya fito takarar kujerar gwamna ne domin a ci gaba da ayyukan cigaba da gwamnatin jihar ke yi yanzu.