[youtube https://www.youtube.com/watch?v=jENha57K7R4&w=760&h=365]
Wasu Mazauna garin Unguwan Boro dake jihar Kaduna sun bayyana ra’ayoyin su kan yadda ake nuna wariya ga masu dauke da cutar Kanjamau.
A tattaunawar da wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA Aisha Yusufu ta yi da wasu daga cikin mazauna wannan unguwa sun bayyana cewa za su ci gaba da zama da abokan zamansu ko da ku suna dauke da cutar kanjamau.
Wasu kalilan daga cik sun ce ba za su ci gaba da zama da abokan zaman su muddun suka kamu da cutar Kanjamu.
Cutar Kanjamau
Cutar kanjamau cuta ce dake karya garkuwar jikin mutum.
Akan kamu da cutar ta hanyar yin jima’i, yin Karin jinin da ba a tabbatar da ingancinsa ba, amfani da rezan da wani ya yi amfani da shi wajen yanke kumba ko al’makashi, wajen yin aski da dai sauran su.
Likitoci sun tabbatar cewa ba a kamuwa da cutar idan an ci abinci tare, ko an tafa hannun da mai dauke da cutar.
Jami’an asibitin sun ce juriya wajen Shan maganin cutar da yin gwajin cutar na cikin hanyoyin dakile yaduwar cutar.
Yin amfani da kororon roba wajen yin jima’i, guje wa amfani da reza ko almakashin mutane, gwada jini kafin a kara wa mutum na cikin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
A Najeriya sakamakon binciken da hukumar NACA ta fitar ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 ne ke dauke da kanjamau a kasar nan.