Tsohon dan wasan super Eagles Kingsley Obiekwu ya gargadi ‘yan wasa da su rika yin tattali saboda gaba.
Obiekwu ya fadi haka ne a lokacin daya ke mika godiyar sa ga Ahmed Musa bisa gagarimar goma ta arziki da yayi masa.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin gagarimar kyuatar da Ahmed Musa yayi wa dan wasa Obiekwu.
” Obiekwu ya shaida cewa wata gidan Radiyo ne ta kira shi cewa wani na son yin magana da shi. Daganan sai aka bashi waya, ansawar sa ke da wuya sai yaji ashe Ahmed Musa ne, sai ya ce masa ‘yan wasan Super Eagles za su yi wani abu akan matsalar da yake ciki amma kafin nan ya na son ya aika masa da lambar asusun bankin sa.
” Bayan awa daya sai kawai na ji alat din naira miliyan 2 sun dira cikin asusun banki na. Na ji dadin wanna taimako daga Ahmed Musa.
Daga nan sai ya yi kira ga sauran tsoffin yan wasa da suka buga wa Najeriya kwallon kafa su fito su bayyana wa duniya halinda suke ciki.
” Ina son in gaya muku cewa akwai iri na da yawa da ke cikin mawuyacin hali. Ko ciyar da iyalan su ba su iya yi saboda talauci. Ina kira ga resu da su fito su bayyana wa jama’a matsalolin su domin a taimaka musu. Yin shiru ba zai yi maganin halin da suke ciki ba.