Shugaban NNPC Mele Kyari ya bayyana cewa dillalan fetur ɗin da suka shigo da gurɓataccen fetur a Najeriya, sun ce ba za su ɗauki asara, alhaki ko laifin shigo da man a cikin Najeriya ba.
Kyari ya yi bayanin ne a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya Kan Man Fetur a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa dillalan fetur ɗin sun ce ba za su ɗauki asara ba, saboda irin wanda NNPC ta ce su sayo, shi su ka sayo.
A makon jiya ne Kwamitin Majalisa ya bada umarnin a yi binciken yadda aka shigo da gurɓataccen mai.
Sannan kuma Majalisar ta umarci NNPC ta dakatar da lasisin shigo da mai na MRS, Emadeb/Hyde/A.Y Maikifi/Brittania-U Consortium Oando da Duke Oil, saboda laifin shigo da gurɓataccen mai.
Ɗan Majalisar Tarayya Mohammed Monguno ne ya bayar da shawarar kuma aka amince.
Tun bayan bayyanar gurɓataccen fetur ɗin ne NNPC da dillalan man su ka riƙa zargin juna, da kuma ƙoƙarin ɗora wa juna laifi.
Kyari ya ce dillalan fetur ɗin sun ce irin wanda NNPC ta ce su shigo da shi, shi ne ɗin su ka shigo da shi.
Sun kuma haƙƙaƙe cewa NNPC ba ta yi binciken duba ingancin man ba.
“Sannan kuma Kyari ya ce dillalan ba su yi binciken ingancin sa ba, don haka laifin masu lodin ne kenan. Don haka a hannun su gurɓataccen ya fito. Don haka ba za su ɗauki asara ba.
Shigo Da Gurɓataccen Mai: Wa Gwamnatin Buhari Za Ta Hukunta Kenan?:
Cikin makon jiya ne Shugaba Buhari ce masu hannu wajen shigo da gurɓataccen mai za su girbi abin da su ka shuka.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana tare da bada umarni a ranar Alhamis cewa dukkan masu hannu wajen sarrafawa da kuma sayo gurɓataccen mai da kawo shi cikin Najeriya, sai sun ɗanɗana aibin abin da suka aikata, daidai abin da doka ta tanadar kan su.
Tun a ranar Laraba ce dai Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a gudanar da bincike, wanda a ranar Alhamis aka bayyana cewa su Oando, A.Y Maikifi, Duke Oil da wasu kamfanoni ne suka shigo da gurɓataccen man daga Tashar Jiragen Ruwa da ke Antwerp, ƙasar Belgium.
Wannan matsala dai ta haddasa ƙarancin mai, domin sai da ta kai an janye kusan lita miliyan 100 daga hannun masu gidajen mai da kuma daffo-daffo.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
“Dangane da batun ƙarancin fetur da ya faru sanadiyyar shigo da wani gurɓataccen mai, Shugaba Buhari ya ce kare lafiya da muradin kwastoma shi ne mafi a’ala ga wannan gwamnati. Din haka za a ɗauki duk wani mataki domin a kare ‘yan Najeriya daga illar amfani da gurɓataccen kaya kowane iri ne.
“Shugaban Ƙasa ya bada umarni cewa a bi duk tsarin da doka ta tanadar wajen gano dukkan asalin yadda lamarin ya faru. Kuma dukkan wanda abin ya shafa na da haƙƙin ganin an saurari koken sa.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa NNPC ta ce ‘Su A.Y Maikifi, Oando da Duke Oil ne su ka shigo da shi daga Belgium’.
Kamfanin Kula da Harkokin Fetur na Ƙasa (NNPC) ya fallasa sunayen kamfanonin dillalan fetur ɗin da suka shigo da gurɓataccen fetur a Najeriya, wanda ake taƙaddama a kan sa.
NNPC ya ce kamfanin harkokin shigo da fetur na Oando, A.Y Maikifi, Duke Oíl, Emadeb da Hyde ne suka shigo da shi, kuma daga Tashar Jiragen Ruwa ta Antwerp, ta ƙasar Belgium.
Shugaban NNPC Mele Kyari ya ce masu duba ingancin fetur sun yi sakacin ƙin duba ingancin fetur ɗin a lokacin da ake sauke lodin sa bakin ruwa.
An dai ƙiyasta cewa gurɓataccen fetur ɗin zai kai lita miliyan 100.
Sanarwar ta ce jami’an NMDRA sun binciki man, amma ba su yi binciken ko akwai man sinadarin Methanol a ciki ba.
Wannan sanarwar ta fito ne kwana ɗaya bayan Karamin Ministan Harkokin Fetur, Timipre Sylva ya shaida wa manema labarai cewa za a yi gagarimin bincike a gano waɗanda ke da hannu a cikin hada-hadar shigo da man.
Discussion about this post