Yin tattaki daya ne daga cikin hanyoyin motas jiki da ke da matukar muhimmanci. Baya ga sauki da yake da shi yana da matukar amfani ga lafiyar mutum.
A dalilin haka likitoci suka yi kira ga mutane da su rika yin tafiya akalla na tsawon miniti 30 a kulum domin inganta lafiyar su.
Ga amfani 16 da tattaki ke yi wa lafiyar mutum
1. Kaifafa kwakwalwar mutum da SA mutum iya yin zurfin tunani.
2. Karfafa kasusuwa inda ko da mutum ya fadi ba zai turgude nan da nan ba.
3. Karfafa gabobbin jiki musamman na kafaffuwa inda rashin yin tafiya ke sa ake yawan fama da ciwon kafa da rashin iya tafiya mai nisa.
4. Kawar da ciwon baya da yawan zama ke sa wa.
5. Kara wa mutum karfi a jiki musamman a wajen yin jima’i da iyali.
6. Rage yawan mantuwa saboda inganta kwakwalwar da yake yi.
7. Inganta garkuwar jikin mutum domin samun kariya daga kamuwa da cututtuka kamar su mura.
8. Kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.
9. Samar da kariya daga kamuwa da cutar siga wato ‘Diabeties’
10. Yin tafiya musamman da dare na taimakwa wajen saurin narkar da abinci
11. Tattaki na rage yawan tunani, damuwa da kwantar wa mutum hankali.
12. Tattaki na taimakwa wajen rage kiba a jiki.
13. Yana taimakawa wajen barci musamman idan barci yana gagara da dare.
14. Tattaki na hana tsufa da wuri. Koda shekarun mutum sun nisa za a ga yana da kuzari a jika.
15. Yin tattaki na taimaka wa mutum samun sinadarin Vitamin D.
16. Ya na taimakawa wajen rage yawan laulayin da mata ke fama da su a lokacin da haila da lokacin da suka kai shekarun daina haihuwa.
Discussion about this post