Barci hanya ce da ke samar wa jiki da kwakwalwa hutu musamman idan an gaji.
Wasu da basu iya yin barci kan yi amfani da magunguna ko su sha shayin da ke sa jiki ya mutu don asamu yin barci yadda ya kamata.
Ilar yin haka shine a duk ranar da mutum bai sha maganin ba ko wannan shayi ba zai iya yin barci ba.
Likitoci sun ce rashin samun isasshen barci kan haddasa haɗarurruka irin na mota, rashin iya yin aiki musamman a wurin aiki, yawan fushi da samun matsaloli a soyayya da zamantakewa a tsakanin mutane.
Rashin samun isasshen barci na haddasa ciwon siga ‘diabetes’, cututtukan dake kama zuciya, damuwa da sauran su.
Abubuwan dake hana mutum barci
1. Yawan yin na hana barci da dare. A rika kaucewa duk wani abu da zai sa rai ya baci a lokacin da za ayi barci.
2. Damuwa: Ya kamata mutane su rika rage yawan damuwa domin guje wa kamuwa da matsaloli musamman tabuwar hankali da rashin iya barci a duk lokacin da aka bukaci haka.
3. Tabuwar hankali: Masu fama da tabuwar hankali na yawan fama da rashin barci.
4. Yawan yin aiki da dare: Aikin dare na hana mutum barci domin dare lokaci ne da ya kamata mutum ya huta.
5. Rashin lafiya ka iya hana mutum samun barci saboda raɗaɗin ciwo.
Likitoci kan hada maganin barci cikin magungunan da ya kamata mara lafiya ya sha domin barci na taimakwa wajen samun sauki.
Hanyoyi 13 da ya kamata a rika kiyayewa domin samun isashen barci
1. A rika kashe wutar lantarki a daki a lokacin da za ayi barci.
2. A daina latse-latsen waya a lokacin da za a kwanta barci. Hakan na sa barci ya gagara.
3. A ɗan yi karatun littafi kafin a kwanta. Shima yana taimakawa wajen samun barci.
4. Za a iya rika yin kirgen wani abu ɗaya bayan ɗaya har barci ya kwashe mutum.
5. Wanka da ruwan zafi ko da na sanyi idan har an ƙasa yin barci na taimakawa.
6. A motsa jiki a lokacin da ya kamata kamar da rana ko safe amma ba lokacin da za a kwanta barci ba.
7. A guji shan giya da cin abinci a tsakiyar dare.
8. Idan za a kwanta barci a tabbatar cewa an samu wurin da bashi da yawan hayaniya ko kara.
9. Kada a yi hiran da ka iya tada hankali a lokacin da za a kwanta.
10. A zabi lokacin da za a rika yin barci da wuri.
11. A rage yawan yin barcin Rana.
12. A rage shan shayin dake dauke da sinadarin ‘nicotine da caffeine’
13. Kada a kwanta da damuwa a zuciya domin yin haka na hana samun isasshen barci.
An wallafa wannan labari a medical news today dake yanar gizo.