Ruɗannin tashin hankali ya sake ɓarkewa a wasu sassan Legas, sanadiyyar mummunan faɗan da ‘yan Ƙungiyar Direbobin Legas ke yi a junan su.
Yawancin kasuwanni sun zama fayau ba kowa, saboda kowa ya arce, ganin yadda ‘yan tasha ke ta shimfiɗar da gawawwaki kwance shame-shame.
Faɗan dai ya faru ne tsakanin ɓangaren ‘yan yuniyal (NURTW) masu adawa da juna a Jihar Legas.
Kasuwannin da aka arce kowa ya tsira da ran sa, sun haɗa da babbar kasuwar Idumota, Kosoko, Tom-Jones da shahararriyar kasuwar Balogun.
Tun a ranar aka fara watsa bidiyon ƙazamin faɗan a soshiyal midiya.
An ga yadda ake ɗaukar matasan da aka ji wa ciwo ana tafiya da su a cikin ‘wheelborrow’, yayin da wasu ke gudu kamar ran su zai fita.
A ranar Talata Rundunar ‘Yan Sandan Legas ta ce ta kama manyan masu hidima biyu na ɓangarorin masu faɗan.
PREMIUM TIMES ta binciko cewa wannan rikici ya bai wa ‘yan fashi damar da suka samu sukunin yi wa ‘yan kasuwa da ‘yan tireda fashi, har ma da kwastomomin da ke zuwa cin kasuwa da masu motocin haya.
Wakilin mu ya gano cewa rikicin ya yi zafi, amma yayin da aka kasa shawo kan lamarin, a ranar Lahadi sai dandazon ‘yan iska da sauran ɓatagari masu garari cikin gari suka hau kan titinan Idumota da kan gadar Idumota ɗin.
Hakan ta sa ‘yan kasuwa sun rufe shaguna su ma ‘yan tireda sun tattara komatsan su sun arce.
Wakilin mu ya ga waɗanda aka ji wa ciwo sosai a kan hanyar Idumota zuwa Mushin.
Wani mai sayar da tufafi a kasuwar Idumota, mai suna Akanni Medigi, wanda aka fi sani da Omojomolo, ya shaida wa wannan jarida cewa an fara faɗan tun a ranar Talata a daidai gadar sama.
Ya ce faɗan ya ɓarke tsakanin magoya bayan Kunle Poly da ‘yan tashar Idumota, waɗanda aka fi sani da ‘Idumota boys.’
Discussion about this post