Yayin da ake cikin tataɓurza kan batun cire tallafin fetur, Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta zargi Hukumar NNPC da zamba da kuma nunke miliyoyin ‘yan Najeriya baibai.
Gwamnonin sun ce muddin ba a gano ko kuma ita NNPC ba ta fito ta bayyana gaskiya abin da ke faruwa ba, to Najeriya za ta ci gaba da tafiya jirkice, kamar mai shan-inna.
Sun faɗi hakan ne a Abuja, yayin ganawar su da shugabannin ƙwadago ɓangaren NLC fa TUC.
Sun yi taron domin tattauna ƙabli da ba’adin da ke tattare da batun cire tallafin mai, wanda suka ce tilas ko badaɗe ko bajima sai an cire tallafin.
Sun yi taron kwanaki biyu bayan Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da cire tallafin.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta ce Buhari ya dakatar da cire tallafin ne, saboda an yi nazarin cewa idan aka ƙara, za a ɗora wa ‘yan Najeriya wahalar da ta wuce wadda su ke ciki a yanzu.
Sannan Zainab ta ce za a zauna da ƙungiyoyi domin a tabbatar cewa idan ma an cire tallafin nan gaba, to ƙarin ba zai shafi rayuwar marasa galihu ba.
An dai daɗe ana kai ruwa rana kan batun cire tallafin fetur.
Yakama Litar Fetur Ta Kai N302 -Majalisar Bunƙasa Arzikin Najeriya:
CIkin watan Nuwamba ne Majalisar Masu Bai Wa Buhari Shawara Kan Tattalin Arziki (NEC) ta bayar da shawarar cewa ya kamata a riƙa sayar da litar fetur ko dai Naira 302 ko kuma abin da ya yi sama.
Sun buga misali da ƙasashen da ke maƙautaka da Najeriya, inda su ka ce idan aka kwatanta da yadda ake sayar da fetur a can, to a nan Najeriya kusan a ɓagas ake shan fetur.
A wurin taron dai Gwamnonin Najeriya sun ce shugabannin da haƙƙin kula da sayar da fetur da masu tara kuɗaɗen sa su na da wani shiri da suke ƙulla zamba a ɓoye, wanda ba su so a gane. Musamman sun zargi NNPC.
Dalili kenan ma a wurin taron Shuagaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi ya yi kira ga NLC da TUC cewa su tashi tsaye su bankaɗo duk wata almundahana da ake tafkawa da sunan tallafin fetur.
Ya ce su gano shin batun tallafin mai da kuma ba a cire ba ɗin, shin lamarin zai amfani ‘yan Najeriya ne baki ɗaya, ko kuwa wasu ‘yan tsiraru ne za su kuɗance a lokaci ƙanƙane.
Idan ba a manta ba, a farkon Disamba Ministan Harkokin Fetur da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele sun ce Najeriya ta dogara ne kawai da matatar Ɗangote, wadda attajirin ya ce zai kammala ginin ta cikin 2022.
Emefiele ya ce idan aka fara tace mai a Matatar Dangote, to Najeriya za ta riƙa sayen fetur a hannun sa da Naira. Maimakon dalolin da ta ke jida ta sayo tataccen fetur a waje, wanda ta ce hakan ne ke sa tilas gwamnati ke kashe kuɗaɗen tallafi kan fetur ɗin.
Discussion about this post