Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta bada sanarwar cewa a cikin watan nan mai kamawa na Fabrairu ne za ta fara horas da kashi na farko na waɗanda su ka amfana da shirin ‘N-Power’ a ƙarƙashin sabon tsarin ta mai suna NEXIT.
A bayanin da ta saki ta hanyar shafin ta na Twitter a daren ranar Asabar, ma’aikatar ta yi kira ga ‘yan Nijeriya waɗanda su ka kammala cin moriyar shirin N-Power da su je su duba cancantar su ta shiga cikin tsarin NEXIT ɗin a cikin mako ɗaya kacal.
Ta ce, “Don Allah a tura text ga wannan lambar *45665# a ranar ko kafin ranar Juma’a, 4 ga Fabrairu domin duba cancantar ka kuma ka nuna ko za ka iya shiga cikin shirin don a yi tare da kai.”
Shi dai tsarin tallafi na NEXIT, an fito da shi ne domin waɗanda aka sallame su daga shirin ‘N-Power’ kuma zai samar da horaswa da kuɗaɗe don mutum ya fara wata sana’a ko ya inganta sana’ar da ya riga ya ke yi.
A tuna, a cikin Satumba na 2021 ne aka tsame mutum 390,000 da su ka nemi shiga cikin shirin ma’aikatar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Minista, Sadiya Farouq.
Discussion about this post