Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ya Bayyana cewa gwamnatin su ta APC ta maida hankalin ta kacokan wajen inganta rayuwar al’ummar ƙasar nan, musamman ma talakawa.
Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke wa Ƙungiyar Ƙwararrun Mambobin APC jawabi, lokacin da su ka kai masa ziyara a karshen makon jiya.
Osinbajo ya ce APC za ta ci gaba da tafiya a kan wannan wannan turba da ta ke a kai, ta kyautata wa al’umma, kamar yadda ta faro tun daga asali.
“Wannan jam’iyya ce ta talakawa. Kuma jam’iyya ce wadda dama ita tambarin ta shi ne ganin talaka ya amfana iyar abin da za mu iya samar masu bakin ƙoƙarin mu.
“Dalili ke nan mu ke da manyan tsare-tsaren bunƙasa rayuwar marasa galihu da dama. Shirin SIP da wannan Gwamnantin ta ƙiriƙiro babu wani shiri mai ƙarfin da ya kai kamar sa a Afrika. Wannan kuwa ya wadatar a gane irin muhimmancin da mu ka bai wa inganta rayuwar marasa galihu a faɗin ƙasar nan.
“Jam’iyyar APC ba wai kawai jam’iyyar shiga ba ce don kawai a samu muƙaman siyasa. APC ginshiƙi ce, tubali ne kuma turba ce ta inganta rayuwa da bunƙasa yalwar arziki cikin al’umma.”
Da ya ke jawabi, tsohon Gwamnan Bauchi Isa Yuguda, wanda shi ne shugaban ƙungiyar, ya ce su ƙwararrun da ke cikin APC sun ga ya kamata su tafi tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, a matsayin sa shi ma na ƙwararre a fannin shari’.