Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya sha alwashin cewa lokacin da gogarman ɗan bindiga Bello Turji zai yi mummunan ƙarshe ya kusa.
Turji na ci gaba da kai munanan hare-hare a yankunan Sokoto, duk kuwa da farautar sa da jami’an tsaro ke yi.
Tambuwal ya yi wannan iƙirarin a ranar Asabar, lokacin da ya ke jawabi a taron gaggawa da ya yi da wasu shugabannin al’umma, sa’o’i kaɗan bayan ‘yan bindiga sun kashe wani hamshaƙin ɗan kasuwa, kuma su ka yi awon gaba da mutum biyar a ƙauyen Kurawa, cikin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sokoto.
Tambuwal ya yi ganawar ce da shugabannin yankin Sokoto ta Gabas dangane da hare-haren da ‘yan bindiga ke kai masu babu ƙaƙƙautawa.
Shaidun gani da ido sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa mahara sun kai farmaki a garin Kurawa cikin daren Juma’a, har zuwa wayewar Asabar sa safe.
A lokacin farmakin ne suka kashe wani ɗan kasuwa mai suna Bashar Yellow, a lokacin da ya ƙi yarda a kama shi a tafi da shi.
“Masu garkuwa sun nemi ya bi su, amma sai Yellow ya ƙi. Na tabbata dama can su na ƙulle da shi, domin shi kaɗai su ka kashe garin.” Haka Basharu Guyawa na Rundunar Adalci ya shaida wa wakilin mu a Sokoto.
“Sun kuma ɗauki mutum biyar, waɗanda a cikin su har da matan aure biyu. Mijin ɗaya daga cikin matan da aka arce da su ne da kan sa ya kira ni ya shaida min.”
Wani mazaunin Sabon Birni ya shaida wa wakilin mu cewa ya ga ‘yan bindigar a lokacin da su ke wucewa zuwa hedikwatar ƙaramar hukumar.
“Wallahi na gan su da ido na da safe. Mutane da yawa sun gan su. Saboda haka kada ma wani ya ce mana wai duk an kori ‘yan bindiga a yankin mu. Hare-haren rashin mutuncin sun yi muni sosai.”
Yawancin yankunan da ‘yan bindiga ke kai hari a Sokoto, su na yanki daya ne da Isa, Sabon Birni, Gwaranyo, Raɓa da Wurno. Kuma su ne su ka aka fi kai wa farmaki.
Discussion about this post