Jami’iyyar PDP ta bayyana cewa da ita za a fafata a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Katsina da za a yi a watan Maris ɗin 2022.
Shugaban Jam’iyyar ta jihar Katsina Yusuf Salisu-Magiri ya sanar da haka ranar Lahadi a lokacin da ɗan takarar kujeran sanata na shiyyar Katsina ta Tsakiya Sirajo Aminu ya ziyarce shi.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Aminu ya je sakatariyar jam’iyyar ne domin sanar da shiyyar, shugabannin kananan hukumomi da jihar gaba daya kudirinsa na tsayawa takarar kujerar sanatan Katsina ta tsakiya.
Salisu-Magiri ya tabbatar cewa wannan karo jam’iyyar na da amintattun mutanen da za su tsaya takarar kujerun shugabanin kananan hukumomi da kansiloli a jihar.
Bayan haka shugaban Jam’iyyar ya yi korafi ga sanarwar da gwamnan jihar Aminu Masari ya yi tun daga farko game zaben kansiloli, inda ya ce hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ce kadai ke da hurumin bayyana hakan.
Salisu-Magiri ya yi kira ga gwamna Masari ya mai da hankali kan ayyukansa kamar yadda doka ta tanadar, sannan ya kara da cewa idan har aka ba shi damar bayyana lokacin yin zabe, yana iya karasa bayyana wadanda suka yi nasara a zaben maimakon hukumar zabe.
Ya ce gwamnan zai iya amincewa da tsare-tsare da kasafin kudin zaben da hukumar zabe ta gabatar ne kawai, ba ya fara gudanar da aiyukkan hukumar ba.
Ya ce, “PDP babbar jam’iyya ce ta kasa. Don haka babu wani zabe da doka ta shirya da PDP ba za ta shiga ba, tabbas za mu shiga.”
Salisu-Majigiri ya ce fitowar da magoya bayan jam’iyyar suka yi domin nuna soyayyar su ga dan takarar, alama ce na hadin kai da kuma samun nasara ga jam’iyyar.
Shugaban na PDP ya hori magoya bayan jami’iyyar da su kara hada kai da jajircewa domin samun nasara a zaben kananan hukumomi da kuma babban zaben 2023.
Discussion about this post