Ma’aikaciyar jinya a fannin yi wa mata masu ciki awo a asibitin St. Lukes dake Wusasa Zariya Elizabeth Peters ta yi kira ga mata musamman masu ciki da su bi a hankali wajen shan zobo alokacin da suke da ciki domin shan zobo ga mace mai ciki na sa ta iya yin barin cikin.
Elizabeth ta ce zobo kan sa mace mai ciki yin bari musamman idan cikin bai yi kwari ba.
Ta ce kamata ya yi mace mai sabon ciki ta hakura da shan zobo har sai cikin nata ya yi kwari sosai kamar wata 8 ko 9 domin a lokacin idan ta sha zobo zai taimakawa wajen fitar da datin dake ciki kafin da ya fito da rage hawan jini.
” Shan zobo ga mace mai tsohon ciki na taimakawa wajen inganta lafiyar ta da dan dake cikinta domin yana kare mace daga kamuwa da hawan jini.
Elizabeth ta kuma ce yin bari bayan an sha zobo ba kowace mace mai jaririn ciki ke samun wannan matsala ba domin mata da dama basu da sanin cewa zobo na iya yi wa mace lahani irin haka ba.
A dalilin haka take kira ga mata da zaran ciki ya shiga su rika kula da abincin da suke ci domin guje wa afkawa cikin matsaloli irin hakla kafin su haihu.
Wani Likita mai suna Udomoh ya gargadi mata masu ciki da su nisanta kansa daga shan Zobo a lokacin da suke da ciki.
Bincike ya nuna cewa akwai alamun cewa zobo na sa wasu dabobbi masu ciki yin bari.
A dalilin haka likitoci ke kira ga mata da su rika nisanta kan su da kwankwadan zobo idan suna da ciki.
Wata ungozoma dake aiki da asibitin Novelty a Abuja Grace Odoma jaddada wannan gargadi da likitoci ke yi game da kwankwadan zobo.
Grace ta ce zobo na dauke da sinadarin dake sa mahaifar mace ya bude.
Ta ce hakan ya nuna cewa idan har mace mai ciki ta yawaita Shan zobo za ta yin bari.
Grace ta Kuma ce zobo na dauke da sinadarin oestrogen wanda ke wanke wa mace ciki.
Ta ce bayan yin bari, sinadarin Oestrogen kan sa a haifi dan da bashi da nauyi sosai.