A ranar Juma’a ne kotun gargajiya dake Igando jihar Legas ta warware auren shekara 12 saboda matar mai suna Rashidat Ogunniyi ta yi korafin cewa mijita Kazeem Ogunniyi ya fi daraja karyarsa da yake kiwo fiye da ita.
Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya raba auren saboda rashin zuwa kotun da Kazeem ya ki yi duk da sammacin da aka aik masa.
Kotun ta bai wa Rashida izinin kula da ‘yar su daya da su suka haifa tare sannan Kazeem zai rika biyan naira 10,000 duk wata domin ciyar da ita.
Koledoye ya ce Kazeem zai dauki nauyin biyan kudin makaranta da sauran bukatun yarinyar.
Idan ba a manta ba a watan Disembar 2021 PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin karar da Rashidat mai shekara 40 ta kai kotu tana rokon alkali ya raba aurenta da mijin ta saboda son karyar sa da yake fiye da itya.
Ta ce tun da ta auri Kazeem kwanciyar hankali ya kare mata kwatakwata.
“Haka kawai idan Kazeem ya bushi iska sa ya rika jibga ta akan abinda bai taka kara ya karya ba saboda kawai son zuciyarsa.
“Akwai ranar da yayi min dukan tsiya a bainar jama’a ya yayyaga min riga kuma bai yi ko nadama ba.
“Wata rana Kazeem ya kwaso kayan sawa ta zai kona, in banda baki da limamin masallacin unguwan mu ya saka ba ya hanashi da shi kenana sai dai in nemi wasu kayan ba wadanda nake da su ba.
Ta roki kotu ta raba auren sannan ta bata izinin rike ‘yar su.
A lokacin alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya dage shari’ar zuwa ranar 18 ga Janairu.
Discussion about this post