Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kamfanin jaridar Thisday dake unguwar Utako Abuja
Jaridar ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ƴan bindigar wanda sun kai su 9 sun afka ginin jaridar kuma sun ɓarnata wasu daga cikin kayan aiki da cin zarafin wasu ma’aikata dake aiki a cikin ofishin a wannan dare.
Shugaban kamfanin na Abuja, Iyobosa Uwugiaren Iyobosa ya bayyana cewa tuni sun sanar wa rundunar ƴan sanda dake Jabi domin bin a bi sawun su.
Sannan ya karyata kalaman ƴan sanda da suka ce wai akwai yiwuwar ƴan fashi da makami suka afka wa kamfani.
” Idan da ƴan fashi ne ai da sun saci wasu abubuwan amma kuma basu yi hakan ba sai kawai suka fice ta inda suka shigo babu satar da suka yi.
Idan ba a manta ba a 2012, ƴan bindiga sun tada bamabamai a ginin ofishin jaridar dake Abuja da Kaduna.
Discussion about this post