Akalla mutum uku ne suka gamu da ajalin su sannan wasu da dama suka ji rauni a batakashin da aka yi tsakanin makiyaya da manoma a karamar hukumar Kirikasamma dake jihar Jigawa.
Darektan yada labarai na karamar hukumar Kirikasamma Sunusi Doro ya sanar cewa gwamnati da jami’an tsaro sun tabbatar da dawowa da tsaro a karamar hukumar.
Doro ya ce rikicin ya auku ne a kauyukan Madaci da Iyo.
Wani mazaunin karamar hukumar Idris Madaci ya bayyana cewa rikicin ya samo asaline a dalilin afkawa gonakin mutane da wasu makiyaya suka yi da shanun su.
Madaci ya ce ganin haka ya sa manoman suka fito domin kare amfani gonakin su.
Ya ce makiyaya sun far wa manoman da kibiya da adduna inda mutum uku suka mutu sannan wasu suka ji rauni.
“An kashe Abba Ali da Umar Sani a kauyen Madaci sannan da Aliso a kauyen Iyo da ya zo aiki daga karamar hukumar Kazaure.
Madaci ya ce an kai wadanda suka ji rauni asibitin Nguru dake jihar Yobe, asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kan dake jihar Kano da asibitin Hadejia.
Ya ce asibitin Aminu Kano na bukatan a biya Naira 300,000 kafin su fara duba mutanen da aka kai asibitin.
“Muna kokarin hada kudaden ne domin ganin likitoci sun duba su.