Kyautar Ballon D’or dai kyauta ce da wata mujallar ƙasar Faransa ke shiryawa, ake bayarwa ga ɗan wasan da ya fi zaƙaƙuranci a kowace kakar wasan wasan ƙwallon ƙasa ta ƙasashen Turai.
Kyautar wadda aka fara cikin 2000, ta bana ta zo da ƙorafe-ƙorafe, musamman ganin yadda aka bayar da kyautar Leonel Messi, wanda ake ganin ba shi ne ya fi cancanta ba.
Robert Lewandowsky na Ƙungiyar FC Bayern da aka ɗauka cewa shi zai lashe kyautar, ya zo na biyu.
A shekarar 2020 Lewandowsky ne kowa ya bai wa kyautar, amma sai aka samu akasi, ba a shirya gasar a 2020 ɗin ba, saboda ɓarkewar cutar korona a duniya.
A ta 2021 da aka bayar kwanan nan a Paris, har yau miliyoyin mutane ba su daina cewa an yi wa Lewandowsky rashin adalci ba. Wasu da dama na cewa kyautar ba ta da sauran wata martaba kenan a duniyar ƙwallon ƙafa.
Ya Ake Zaɓen Gwarzon Ballon D’or?
‘Yan jarida ne masu rubutu da sharhin ƙwallo ke zaɓen wanda ya zo na farko. Daga cikin waɗanda aka fitar ne ake zaɓen wanda ya fi kowa yawan ƙuri’u.
Leonel Messi: Ya samu ƙuri’u 613.
Lewandowsky: Ya samu ƙuri’u 580.
Bajintar Messi Da Lewandowsky Cikin 2021 A Faifai:
Leonel Messi: Ya yi wasanni 56 daga Janairu zuwa Oktoba. Ya ci ƙwallaye 41. Ya lashe kofi biyu.
Lewandowsky: Ya buga wasanni 54, ya ci ƙwallaye 64, ya haura Messi da ƙwallaye 23 kenan. Sannan kuma ya ci kofi 4 duk a cikin 2021.
Idan kuma aka auna Messi da Lewandowsky tun daga shekarar 2020 wadda ba a bayar da kyautar ba har zuwa yanzu da aka yi bikin bayar da ita cikin Nuwamba, za a ga Messi ya ci ƙwallaye 67 kaɗai, yayin da Lewandowsky ya ci ƙwallaye 101.
Kenan, banda Lewandowsky, Ronaldo da Rumelu Lukaku duk sun fi Messi cin ƙwallaye daga 2020 zuwa 2021, lokacin da aka yi zaɓen kyautar. Ronaldo na da 82, Lukaku na da 70.
Sai dai a wannan shekarar, an fito da wata kyauta ta Gwarzon Ɗan Gaba, wadda aka bai wa Lewandowsky ɗin.
A lokacin da Messi ya karɓi kyautar sa, ya jinjina wa kan sa cewa ya yi alfaharin yin takara da Lewandowsky. Messi ya ce Lewandowsky haziƙi ne. Sannan kuma ya ce, “A gaskiya Lewandowsky ya cancanci kyautar Ballon D’or ta 2020, wadda ba a samu damar bayarwa ba. Ina fatan masu shirya wannan kyautar za su bi shi har gida, su ba shi abin sa.”
Laifin Me Mendy Golan Chelsea Ya Yi Aka Hana Shi Kyautar YASHIN A Bukin Ballon D’or?
A wurin bada kyautar Ballon D’or, an bai wa ɗan wasan mai tsaron gidan AC Milan wanda ya koma PSG, wato Dunnarumma Kyautar Yashin.
Hatta abokan adawa na ganin mai tsaron gidan Chelsea ne Mendy, ya fi cancanta a ba shi kyautar, ba Dunnarumma ba.
Bajintar Mendy Da Dunnarumma A Kan Faifai:
Mendy: Ya buga wasa 50, an zura masa ƙwallaye 27. Ya yi wasa 29 ba tare an jefa masa ƙwallo ko ɗaya ba. Ya ci kofuka 2.
Dunnarumma: Ya yi wasanni 53, an zura masa ƙwallaye 49. Ya buga wasanni 22 ba a zura masa ƙwallo ba. Ya ci kofi ɗaya tal.
Kyautar Yashin: An bai wa Dunnarumma.
Mai karatu sai ka yi alƙalanci.
Discussion about this post