Hukumar NYSC ta bayyana cewa daga Janairun 2022 daliban da suka yi allurar rigakafin korona ne kawai za a bari su yi wa kasa hidima a Najeriya.
Shugaban hukumar Brigediya Janar Shuaibu Ibrahim ya fadi haka wajen kaddamar da dalibai masu yi wa kasa hidima na rukunin dalibai na C ranar litinin a Abuja.
“Domin ci gaba da kiyaye sharuddan kaucewa kamuwa da cutar korona hukumar NYSC za ta rika daukar wadanda aka yi wa rigfakafine kawai, wato wadanda suka nuna shaidar yin allurar rigakafin korona kafin a barsu su shiga sansanain masu bautar kasa.
Ibrahim ya ce hukumar ta dauki wannan mataki ne domin dakile yaduwar cutar da kuma kiyaye wadanda basiu da ita.
Bayan haka Ibrahim ya hori ‘yan bautan kasa su maida hanklali wajen horo da za a basu na koyan sana’o’i da z a ayi musu a lokacin aikin hidima wa kasa.
Discussion about this post