Babban kalubale wanda a kullum yake addabar shugabannin Nijeriya, musamman a fannin tattalin arziki, bai wuci ta yadda bunkasar tattalin arziki wanna kasar baya tasiri a rayuwar talakan Nijeriya ba, ko nawa girman tattalin arzikin nijeriya ya kai wato GDP ba a ganin wani chanji a wajen talakan kasar nan. Kai duk lokacin da a kace man fetur ya tashi a kasuwar duniya tofa shi kuma tallakan Nijeriya ya shiga tashin hankali da jimamin za a kara masa firashi man da yake saya.
Wai shin kuwa gwamnatin Baba Buhari da hukumomin tattalin arziki na duniya suna nazari kuwa a kan yadda rayuwar talakawan Nijeriya take, kafin tursa sa su akan wata manufa akan arzikin kasarsu? Koda ance ana saida man fetur da araha a Nijeriya sabanin sauran kasashe masu arzikin man fetur, to yana da kyau ayi la’akari da talauchin da yayi way an kasar katutu.
A misali, bincike ya nuna duk duniya dan Nijeriya ne kadai ya kan kashe kusan duk abin da ya samu akan abinci, saboda tsananin talauchi. Matsakaicin mutum dan Nijeriya yakan kashe kashi 65% na kudin da ya samu wajen sayen abinci kadai, wanda wannan yake kara tura yan kasar cikin kangin talauchi. Amma a kasashe kamar Amurka su kan kashe 6.4%, Birtaniya 8.2%, Canada 9.1%, Australia 9.8% kacal ne a kan abinci. Da wuya wani yace an yid an Nijeriya adalchi in har aka hada shi da irin wannan kasashe wajen sayen arzikin da ke kasarsa. Shi kansa Bankin Duniya (World Bank) a wannan shekarar ya fidda kididdiga cewa farashin abinchi a Nijeriya ya karu da 22%, wanda ya sake sanya al’umma cikin talauci.
A bangren sufuri kuwa, wanda ke zaune a kasar England zai iya zuwa yayi aiki a kasar Germany ko France ko Belgium ya dawo ya kwana a gidan sa, ta hanyar jirgin kasa, amma a Nijeriya babu kykyawan tsari na sufuri, misali daga Kano zuwa Legas ko Abuja ko Patacol. Yan Nijeriya sun fi kowa mutuwa a duniya ta hanyar hatsarin mota, sakamakon yin amfani da kana motocin da bai kamata a yi sufuri da suba. Talauchi da rashin kudi kan sanya pasinjoji cunkusuwa sama da mutane gome a mota mai cin mutun hudu kachal, amma a kasashen da suka da kyakkyawan shugabanci sun tanaji motoci na sufuri don kaucewa hatsura.
A duk masu arzikin man fetur a duniya, kama da kasashen da ke cikin kungiyar OPEC Nijeriya ce kadai bata iya tace man fetur a kasarta, wannan ba komai bane face gazawar shugabanci da shugabanni. Shekaru da yawa Nijeriya ta samu kanta cikin matsalar tacewa da sayar da man fetur, kasancewar yana da ga cikin babban abun bukata ga yawan al’ummar wannan kasar, kasancewar babu kyawawan tsari da shugabannin kasar nan suke samar a fannin tattalin arziki da kawar da talauchi a tsakinin yan kasa, babban al’amari ma babu wani kykkyawan tsari na sufuri, wanda shine ganshiki amfani da man fetur.
Matsalar man fetur da tallafin man fetur ya zama wata siyasa da masu neman mulki ke amfani da shi wajen neman a zabesu, wanda kawai ana kokuwar neman iko ne ba tare da shirin warware wannan matsalar ba, da zarar an samu nasara, sai a dulmiya cikin matsalar fiye da ta baya, ana maganin kaba kayi na kumbura.
Gwamnatin shugaba Buhari da jama’iyar APC, sun sami galabar cin zabe a shekarar 2015 ne, bisa yayatu tabbarbarewar tsaro da kuma yunkurin cire tallafin man fetur da gwamnatin PDP da shugaba Goodluck Jonathan tayi yunkurin yi a wannan lokacin a shekara ta 2012. A wannan lokacin kungiyar ‘Yan Kwadago sun jagoranci zanga-zagar da ake kira ‘Occupy Nigeria’ wanda harda shugaba Buhari da sauran jagororin jami’iyun adawa a wannan lokacin sun hallata, kuma wannan bijerewar ta yan kasa ta hana kara kudaden man fetur din. Amma da Buhari yahau mulki, me ne ne ya biyo baya?
Wai ma yasa ne, kowane lokaci kasashen turawa da hukumomin su irin su IMF, basa kawo wa Nijeriya wani tsari ko tilasta su akan wani tsari, sai lokacin da kasar take kan wani bigire na rashin zaman lafiya? Ko kuma sai muna daf da mu shiga zabe, duk da sun san cewa, wannan tsarin zai iya kawo fitina, koma ya sanya kasar cikin wani yanayi.
A shekarar 2012 Nijeriya na tsaka da fitinar Boko Haram an samu irin wanna yanayin na cire tallafi da kara kudin mai, kamar yadda na fada a sama, wanda da kyar kasar nan ta sami kanta, har ma wasu turawan na harsashen bajewar kasar kafin zaben 2015, amma Allah ya karyata su.
Wai wace ce hukumar IMF ne, wanda shugabannin muke tsoro kamar Allah, wanda kullum tsare tsarenta ya kan sake dunkufar da talaka ne kawai, sannan ya share musu hanyar sake mallakar mu ta fuskar tattalin arziki.
A takaice wannan hukuma ta IMF an samar da ita ne bayan an gama yakin duniya na biyu (second world war), Kasar Amurka da kasar Bitaniya ne suka kan gaba wajen kafa wannan hukumar da takwararta ta World Bank, wanda ita hukumar IMF tafi maida hankali wajen sanya wa kasashe ka’idodi na tafikad da tattalin arzikinsu wanda zai dace da muradin kasar Amurka, wato economic policies.
Babban Ma’ajin Amurka (US Treasury Secretary) Harry Dexter White da kuma masanin tattalin arzikin kasar Birtaniya wato John Maynard Keynes, wanda kowanan su ya wakilci kasar sa, su suka tsara da samar da wadan nan hukumomi na IMF da World Bank.
A takai ce wannan hukuma ta IMF babbar makiya ce ga kasashe masu tasowa, musamman na Africa domin yi tarnaki na bunkasa tattalin arzikin su dama barin su su zau na lafiya, ta hanyar kawo musu tsare-tsare da ya sabawa muradun al’umar su.
IMF ta kasance kamar yar sandar duniya ta fnnin tattalin arziki, musamman ka kasashe na bakar fata. Wannan hukuma kawai tanayiwa kasar Amurka ne aiki, wannan ya sanya basa kula da yadda kasa ta ke ciki wajen tilasta musu bin tsari da bai dace da suba.
A wani hannun su kuma shugabannin mu, suna da lalaci, rashin kwarewa a kan matsalolin al’umar su, musamman a fannin tattalin arziki da bunkasa shi. Shugabannin kasashen mu sun fi son mulki da dawamma a kan mulki fiye da bautawa al’umar su, sun gwamce da sharholiya da kasha kudaden talakawa a kan biyan bukatun su, maimakon gina musu kykkywan tsari don yaye musu talauchi da samar musu yalwatacciyar rayuwa.
Ba kawai hukumar IMF fa, it ma sabuwar dokar man fetur da shugaba Buhari ya sanya wa hannu a wannan shekarar wato Petroleum Industrial Bill (PIA), kusan ta damula siyasar tallafin man fetur, wanda wannan dokar ta bayan gida ta cire hannun gwamnati akan harkar man fetur, yadda a yanzu hukumar NNPC ta koma NNPC Limited, wanda ko da a yanzu ta soma ikirarin cin riba, wanda a baya bata iya lissafa riba koma faduwa, wanda a takaice, tabar kasuwa tayin halinta a game da man fetur.
Wannan doka ta nuna cewa a hankali gwamnati zata zare hannun ta a kan man fetur a wannan kasar. Wanda wannan ya sanya hukumar NNPC din ta yi nuni da cewa duk mai adawa da cire tallafin man fetur, to ya makara, har su kan su kungiyar ‘Yan Kwadagon, domin sunce da basu bari an aiwatar da dokar ba tun daga majalissar dokoki ta kasa, kafin ta samu sahalewar shugaban kasa. Wanda yanzu suna ganin karshen tika tika tik, akan cire tallafin man fetur.
Koma bai ke faruwa ya kamata Shugaba Buhari ya tuna alkawarin sa da talakawan Nijeriya, wanda su su ka kawo shi kan mulki, bacin yayi karo biyar yana faduwa, na rage musu kuncin rayuwa da basu zaman lafiya. Ya kuma zama dole mahukunta suyi nazari da kasar su, al’umar su kafin kawo ko wane tsarin musamman a irin wannan lokaci.
alhajilallah@gmail.com