Wani gini mai hawa 21 ya ruguje a garin Ikoyi na jihar Legas.
Ginin da ke lamba 20, Gerrard Road, ya ruguje da misalin karfe 3 na rana, ranar litinin.
Mukaddashin kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da rugujewar wannan bene.
Farinloye ya kara da cewa jami’an hukumar NEMA sun dunguma zuwa wannan wuri da hadarin ya auku.
Ba a dai san adadin yawan wadanda suka mutu sakamakon rugujewar ginin ba da kuma nawa ne suka makale cikin ginin.
Discussion about this post