Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Anambra Jide Onyekwulu ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar wa mutane tsaftataccen ruwan sha domin dakile bullar Kwalera a jihar.
Onyekwulu ya fadi haka ne da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Litinin a garin Awka.
Ya ce bai kamata gwamnati ta rika jira sai cutar ta bulla a jiha ba kafin ta rika fadi-tashin nemo magani da dakile shi.
“Samar wa mutane musamman a yakin karkara tsaftataccen ruwan sha zai taimaka wajen hana bullar cutar a jihar.
Onyekwulu ya ce NMA a shirye take ta hada hannu da gwamnati domin hana bullar cutar da wasu cututtukan.
Idan ba a manta ba hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa cutar kwalara ta yi ajalin mutum hudu sannan ana yargin wasu mutum 78 sun kamu daga ranar daya zuwa bakwai ga Nuwanba a jihohi shida a kasar nan.
Wadannan jihohi sun hada da Barno, Kebbi, Adamawa, Oyo, Ogun da Rivers
Zuwa yanzu cutar ta kashe mutum 3,449 sannan ana zargin mutum 100,057 sun kamu da cutar a kasar nan.
Ga abubuwa 10 dake haddasa barkewar Amai da Gudawa
1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.
2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.
3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.
4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.
5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.
6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.
7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.
8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.
9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.
10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.