Kwamishina Kasafin Kudin jihar Kaduna, Mohammed Abdullahi ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, jihar Kaduna za ta rika tara kudin da zai rika biya mata bukatun kasasfin kudinta na kowacce shekara.
Abdullahi ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar a wajen zaman kare kasafin kudin jihar wanda gwamnatin jihar ta mika wa majalisar a cikin watan jiya.
” Mu a jihar Kaduna burin mu shine mu tara kudin da zai iya biya mana bukatun kasafin kudin mu na kowacce shekara ba sai mun jira kudi daga gwamnatin tarayya ba. Wannan shine burin mu kuma muna gab da mu cimma sa.
” A jihar Kaduna kashi 31 ne cikin 100 muke amfani daga rabon mu na gwamnatin tarayya amma sauran kashi 69 cikin 100 na dawainiyar kasafin kudin jihar duk daga harajin da muke tarawa ne muke amfani da su wajen ayyukan da ke kunshe a kasafin kudin jihar.
” A lokacin da wannan gwamnati ta dare mulki, naira biliyan 13 kacal ake iya tara wa daga haraji, amma yanzu muna tara akalla naira biliyan 57 duk shekara.
” Akwai wasu jihohi da ma’aikatan su ke bin su bashin albashi na tsawon watanni 5-8 saboda dogaro da kudi daga gwamnatin tarayya, amma mu a jihar Kaduna sululu yake duk wata kamar hadiye tuwon dawa da miyam Kalkashi.