Mazauna unguwar Gidan Dare da wasu unguwannin da ke cikin garin Sokoto sun koka kan yadda ‘yan bindiga suka addabe su a cikin kwanakinnan.
A ranar litinin, yan bindiga dauke da manyan bindigogi sun dira unguwar gidan Dare inda suka yi artabu da wasu jami’an Sibul Difens har suka kashe daya daga cikin jami’in.
Mazauna sun ce ko da ‘yan bindigan suka shiga unguwar, mutane sun rika arcewa zuwa gidajen su. Wani da ke tsaye a waje ya bayyanawa wakilin PREMIUM TIMES cewa daya daga cikin ‘yan bindigan ya tambayeshi ko yana da karan sigari ya bashi, sai ya ce bashi da shi, daga nan ya kora shi gida.
Shugaban Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa Mustapha Shehu ya jinjina wa kokarin da jam’ian tsaro suka yi a lokacin da yan bindigan suka shigo unguwar.
Sai dai kuma a wajen kokarin kora su daya daga cikin jami’an Sibul Difens ya rasa ransa bayan ‘yan bindigan sun dirka masa bindiga har sau uku a tsakiyar kokor zuciyar sa.
Mazauna wasu unguwannin sun bayyana cewa suma suna fama da hare-haren ‘yan bindigan a unguwannin su.
” Sun matsa mana a cikin kwanakin nan, haka kawai sai muji sun afka mana sun debe mana kayan abinci da na sawa da duk wani abun more rayuwa da suka kai ga.