Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Baba ya ƙaryata wasu rahotannin da ake yaɗawa cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta fitar da mata ‘yan sanda da ke zaune cikin barikonin ‘yan sanda tare da mazan su fararen hula.
Wasu kafafen yaɗa labarai (banda PREMIUM TIMES), sun buga labarin cewa an ba duk wata jami’ar ‘yar sanda da ke zaune a cikin barikin Enugu wa’adin daga nan zuwa watan Janairu, 2022 duk su fice daga cikin barikin.
Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ne ya sanar wa manema labarai hakan, a cikin wata sanarwa da ya watsa a ranar Laraba, a Abuja.
Labaran da aka riƙa yaɗawa dai na ɗauke da sanarwar bai wa jami’an ‘yan sanda mata umarnin cewa duk wacce ke zaune cikin bariki tare da mijin ta, muddun farar hula ne, to ta fita daga cikin barikin, kafin nan da ranar 31 Ga Janairu, 2022.
Sufeto Janar Baba ya ce labarin ƙaƙale ne, ƙarya ce, kuma rashin adalci ne ƙarara da nuna bambanci, idan aka kori ‘yan sanda masu auren fararen hula daga cikin barikin ‘yan sanda.
Ya ce ‘yan sanda maza da mata duk ɗaya su ke ga dokar Najeriya, babu wani banbanci.
Usman Baba ya ce sanarwar da wasu suka fitar na shirin fitar da matan daga barikin soja, ƙarya ce, domin ta saɓa wa tsarin aikin ‘yan sanda, wanda ba ya nuna bambaci ko fifiko kan mata, kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.
Daga nan sai ya umarci Babban Jami’in Bincike na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ya gaggauta gudanar da bincike, domin gano ko su wane ne suka buga takardar da ke ƙunshe da sanarwar fitar da mata ‘yan sanda masu auren fararen hula daga cikin bariki.
A ƙarshe ya yi kira ga manya da ƙananan ‘yan sanda baki ɗaya su yi watsi da zance shirin fitar da wasu daga cikin barikokin su.
Discussion about this post