Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya bayyanawa manema labarai a garin Katsina cewa yanzu yan bindiga sun koma yin amfani da na’urar ‘Walkie Talkie’ wajen sadar da sakonni a tsakanin su.
Mustapha ya ce tun da gwamnati ta surfafi yan bindiga suka koma tare hanyoyi da masu babura suna juye man fetur daga tankunan su, suna afkawa kauyuka suna kwace da fashin abinci da kayan sawa.
” Yanzu kuma sun tsiri siyan na’urar ‘Walkie Talkie’ domin isar da sakonni a tsakanin su a cikin dajin. Wannan babban koma baya ne ga kokarin da ake yi na kawo karshen su a jihar da yankin Arewa Maso Yamma.
A karshe Mustaha ya ce duk da haka, gwamnati ba ta yi kasakasa ba wajen farautan wadannan ‘yan bindiga da ke amfani da na’urar ‘Walkie Talkie’ a jihar.
Discussion about this post