Zargi: Wani mai amfani da shafin Twitter na zargin wai darajar kudin CFA daidai ya ke da kudin Najeriya wato naira
Akwai CFA iri biyu, akwai West African CFA franc wadda ita ce takardar kudin kasashen da ke amfani da harshen Faransanci a yankin yammacin Afirka ke amfani da ita, akwai kuma Central African CFA franc wanda kasashen yankin Afrika ta tsakiya, masu amfani da harshen Faransanci ke amfani da ita. Duk da cewa takardun kudin sun banbanta darajarsu daya ne kuma suna da tsayayyen mizanin musaya tsakanin su da takardar kudin euro na Turai.
CFA ta yankin tsakiyar Afirka it ace wadda kasashe 6 ke amfani da ita a karkashin Tarayyar Kudi da Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Tsakiyar Afirka. Ana amfani da alamar XAF domin takaita shi a kasuwanin hada-hadar kudi.
Kasashen sun hada da Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Cadi, Jamhuriyar Kwango, Equitorial Guinea da Gabon.
A daya hannun, West African CFA franc shi ne kudin da kasashe 8 a karkashin Kungiyar Tarayyyar Kudi da Tattalin Arzikin kasashen yankin yammacin Afirka ke amfani da ita. Kasashen sun hada da Benin, Burkina Faso, Cóte D’Ivoire, Guinea Bissau, Mali, Nijar, Senegal da Togo. A kasuwannin hada-hadar kudi, a kan gane shi da alamar XOF.
Bisa bayanan da aka bayar a wani gajeren tarihin da ke shafin Babban Bankin kasashen Yankin Yammacin Afirka (BCEAO), an kirkiro CFA ranar 26 ga watan Disamban 1945 – wato a ranar da Faransa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Bretton Woods ta kuma yi sanarwar farko ta daidaituwa ga Asusun Lamuni na Duniya wato IMF.
Kafin nan, yankunan da ke karkashin mulkin Faransa na amfani da takardun kudin da ke da dangantaka da Franc na Farsansa, amma bayan ‘yancin kai, yawancin kasashen sun daina amfani da kudin na franc: Tunisiya a 1958, Morocco a 1960, Guinea a 1959, Algeriya 1964, Madagascar da Mauritaniya 1973.
Asusun ba da lamuni na duniya ya bayar da gajeren tarihi kan yadda aka rage darajar CFA.
Saboda farashi mai tsadan da ake sanyawa kayayyakin da aka sarrafa a kasashen da ke amfani da CFA ba’a mu su amfani da farashin da zai zo daidai da wadanda ake samu a kasuwannin duniya, saboda haka, tattalin arzikin wadannan kasashen ba su bunkasa yadda ya kamata ba a shekarun 1980 da 1990.
Domin shawo kan lamarin kasashen sun tattauna da juna da IMF da Faransa, daga nan ne aka yanke shawarar rage darajar kudin CFA da kashi 50 cikin 100.
Wannan na nufin cewa daga watan Janairun 1994 darajar CFA 100 ta zo daida da Franc daya na Faransa. Burin rage darajar kudin shi ne maido wadannan kasashe bisa turbar da za ta samar musu da bunkasa mai dorewa ta kuma taimaka musu su yi gogayya da sauran takwarorinsu a kasuwannin duniya. Wannan mataki dai, sai ya fi bayar da karfin gwiwa ga fitar da kayayyaki saboda ya baiwa masu amfani da CFA damar fitar da kayayykinsu a kan rabin farashin da ake samu amma kuma ya bukace su su shigar da kayayyaki a farashin da ya ninka wanda suke fitarwa.
To sai dai a 2019, shugaban kasar Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya yi wani sauyi a dangantakar da ke tsakanin Faransa da Afirka lokacin da ya ce kasashen Afirkan da ke amfani da harshen Faransanci na so su dauki nauyin darajar kudin su kuma a shirye suke su janye wasu daga cikin kaddarorin da suka ajiye a Faransa. Suka kuma ce za su sauya sunan takardar kudin zuwa “Eco”.
Wani mai amfani da shafin tiwita @taiwoainafilms kwanan nan ya wallafa wani zargi a shafin shi mai cewa wai yanzu darajar West African CFA Franc daidai ya ke da Nerar Najeriya. Tuni dai mutane 2,800 suka yaba da labarin kuma har an yada shi sau da yawa a tiwitan.
Mai yiwuwa wannan na da dangantaka da faduwar darajan neran da ake gani kwanan nan. A ranar 6 ga watan oktoba, darajar nera ta fadi sosai da aka kwatanta da dalan Amirka a farashin gwamnati.
Wani rahoton da jaridar Premium Times ta yi amfani da shi ya ce bayanan da aka samu daga FMDQ wadda aka fi sani da Kungiyar masu zuba jari da fitar da kayayyaki inda ake hada-hadar kasuwanni ya nuna cewa dallan Amirka guda shi ne nera 414.73.
Sau da yawa ana danganta faduwar darajar nerar da matakin CBN na dakatar da ‘yan canji daga yin canji a duk fadin kasar.
Ranar 27 ga watan Yuli CBN ta dakatar da ‘Yan canji daga yin sana’ar tana zargin masu sana’ar da kasancewa hanyar fitar da haramtattun kudade da kuma aiki da mutanen da ke karbar cin hanci da rashawa da ma wanke haramtattun kudade a Najeriya. Jim kadan bayan sanarwar darajar nerar ta fadi, aka sayar da dala a kan 503, washe gari kuma ta sake raguwa da dala 2.
Ranar lahadi a hukumance, dala daya na da darajar 410.8. Sai dai farashin ya banbanta da na ‘yan canji tunda su suna sayar da dala daya kan nera 573.
Tantancewa
Daga sakamakon binciken shafukan kudi, Dubawa ta gano cewa darajar CFA da ta nera ba daya ba ne. A kasuwar gwamnati, nera 1 daidai ta ke da Western African CFA franc 1.38 wanda Jamhuriyar Benin ke amfani da shi ke nan.
Wani karin binciken ya nuna cewa darajar kudin daidai ya ke da Central African CFA franc.
Sai dai darajar CFAn ta karu domin nerar da ke kan 1.38 XOF ta kasance kan 3 XOF a shekarar 2015, shekaru 6 da suka gabata.
Dubawa ta sake yin aiki da bayanan da ta samu kan darajar kudaden a shafin hada-hadar kudin Birtaniya, inda ta gano cewa darajar nera ta ragu da kashi 54 cikin 100 a shekaru 6n da suka gabata idan aka kwatanta da XAF da XOF.
Binciken ya nuna cewa ranar 10 ga watan Disamban 2015 3XAF/XOF ya kasance nera daya (1)
A wani rahoto jaridan The Guardian, ta ce darajar kudin nera ta ragu da kashi 108 cikin 100 idan aka kwatanta da CFA tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020. A cewar rahoton, a shekarar 2015 CFA ta fara karfi sosai. Tsakanin watan Ogosta na 2015 zuwa Ogostan 2016 darajar nera ta fadi da kashi 69 cikin 100 kowace shekara.
A karshe
Zargin cewa darajar naira daidai ta ke da ta jamhuriyar Benin wato CFA ba gaskiya ba ne. Alkaluman da aka tanadar a hukumance sun nuna cewa darajar naira na sama da CFA na Benin.