A cikin shekaru 30 da suka wuce akalla gidaje 233 kamfanonin da aka kirkiro su don kauce wa biyan haraji 166 a wasu ƙasashe suka siye su wanda suka kai Fam miliyan 350.
An gano cewa cikin waɗannan kamfanoni 166, 137 na attajirai da masu faɗa aji ne ƴan Najeriya shafaffu da mai.
Sannan an gano cewa an fi tafka waɗannan harƙalla ne a tsakanin shekarun da PDP ke mulki a Najeriya, lokacin mulkin Goodluck Jonathan, daga 2010 zuwa 2015.
Mafi yawa daga cikin harkallar sayen gidajen an fi yin su ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, domin a lokacin an zargi gwamnatin da kyale manyan gwamnati na yin kashe muraba da kuɗaden gwamnati yadda suke so. Sai dai shugaba Jonathan ya kan fito ya kare gwamnatin sa cewa tsaftatacciya ce.
Stella Oduah kadai, ta siya gidaje a birnin Landan har na naira biliyan 5.
Sanatar ta yi amfani da wani kamfanin tsibirin Seychelles, wanda wannan tsibiri wuri ne da ake dasa harkalla hankali kwance ba tare da wani ya ce maka ci kanka ba.
Ta hanyar wannan kamfani da ta rika loda wa kuɗaɗe masu yawa ta siya manyan gidaje a Landan guda hudu da aka yi musu kuɗi a jimlace dukkan su hudun suka tashi kan Fan miliyan 6.7 a tsakanin watan Oktoban 2012 da Agustan 2013.
A lissafe dai yanzu kuɗin gidajen duka huɗu sun tashi akan naira biliyan 5.2, idan aka duba darajar Fan 1 da ya kai naira 775 a kasuwar bayan fage kenan. Idan kuma lissafin ka akan musayar canjin na CBN ne, ₦558, to gidajen zasu tashi akan naira biliyan ₦3.7.
Shi ko Bello Koko wanda shine shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa NPA kusan unguwanni yake siya a Landan.
Koko ya shiga cikin ƙazamar ƙamayamaya da ƙaƙububar satar kuɗaɗen Najeriya ya na kartatar da su waje, inda ya ke sayen maka-makan gine-gine da kadarori a birnin Landan.
A ƙarƙashin wannan harƙalla, ya riƙa yin shigar kare-da-fatar-akuya da sunan wasu kamfanoni biyu na Shell, ya riƙa danƙara kuɗaɗen da ake sayen kadarori a Landan.
Gungun ‘yan jarida masu yaƙi Da ɓarayin kuɗaɗen gwamnati a duniya ne su ka bankaɗo wannan ƙazamar harƙallar da ake kira ‘Pandora Papers’.
Bello Koko tare da matar sa mai suna Agatha Anne Koko, sun yi amfani da wani kamfanin ɓoye sirrin maɓarnata, Cook Worldwide and Alemin, su ka yi rajistar kamfani a asirce ta hanyar ɓoye sunayen su, aka sa sunayen bige a matsayin masu kamfanin.
An raɗa wa kamfanin suna Coulwood Limited, mai rajista lamba 1487897.
Discussion about this post