Ƴan bindiga sun kashe mutum 10 a hari da suka kai kauyen Yasore dake kusa da garin Batsari jihar Katsina.
Wani mazaunin garin Yasore, Harisu Hamza ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun afka garin ne a bisa babura suna harbi ta ko’ina.
” A wannan harbi suka kashe mutum 10, suka kuma ji wa wasu da dama rauni.
” Akalla maharan sun shigo garin bisa babura 20 ne kuma dukkan su rike da bindiga kowa yana wa duk abinda ya gani gaban sa mutum ne, dutse ko ma Aljan, kiliya da madarar luguden wuta.
Hamza ya ce bayan kisar mutane da suka yi sai suka kuma farfasa shagunan mutane suka kwashi kayan abinci kafin suka fice a garin.
” “Maharan sun dibi kayan abinci da abubuwan amfani na mutane. Tun byan sallar Asuba suka shiga garin ba su fice ba sai bayan karfe 10 da wasu mintoci sannan suka arce.
A wannan lokaci ne yan banga da jami’an tsaro suka shigo isa garin.
Discussion about this post