Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta ceto mutum 187 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.
Kakakin rundunar Muhammad Shehu ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Gusau.
Shehu ya ce rundunar ta ceto wadannan mutane a can cikin dajin Tsibiri dake karamar hukumar Maradun.
Ya ce a cikin mutanen da aka ceto akwai maza da mata da kuma yara kanana.
“Ga dukan alamu wadannan mutane sun dade a hannun ‘yan bindigan da suka kama su amma yanzu haka mun damkasu a hannun gwamnati.
“Mun Kuma gano bayan bincike cewa wadannan mutane a sace sune a kauyukan Rini, Gora, Sabon Birni, Shinkafi wansa suna karkashi kananan hukumomin Bakura, Maradun da Shinkafi ne.
Elkanah ya kara da cewa tuni an damka su ga gwamna Bello Matawalle.
Da yake jinjina wa kokarin da jami’an tsaron suka yi gwamna Matawalle wanda sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe ya wakilta ya ce gwamnati za ta ci gaba da mara musu baya don ganin tsaro ya tabbata a Jihar.
Balarabe ya ce bayan likitoci sun duba su za mika kowa ga iyayen sa da yan uwa.
Ana samun nasarori sosai a ayyukan gamawa da ƴan bindiga da jami’an tsaro ke yi a fadin jihar.
Discussion about this post