Gwamna jihar Kebbi Atiku Bagudu na ya yi alwashin kawo karshen matsalar rashin tsaftacaccen ruwan sha a jihar kafin ya kammala wa’adin mulkin sa a 2023.
Bagudu ya bayyana haka ne a jawabin da yayi bayan ya ziyarci hukumar samarda ruwan sha ga birane da karkara ta jihar, RUWASSA a Birnin Kebbi.
Gwamna Bagudu ya ziyarci hukumar ne domin duba kayan aikin haƙa rijiyoyin burtsatse a fadin jihar.
Bagudu Wanda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Suleiman Muhammad-Argungu ya wakilta ya ce samar da tsaftataccen ruwan sha a duk fadin jihar na daga cikin matsalolin da gwamnati ta maida hankali akai don kawar wa.
Argungu ya ce gwamnati ta dauki wannan alkawari bayan kukan dagacen wata kauye ya yi a lokacin da suka kai ziyara garin.
” A baya gwamnati ta bada kwagilolin haka rijiyoyin burtsatse a wasu kauyuka a jihar amma sai aka samu matsalar rashin ruwa bayan an haka rijiyoyin.
“Hakan yasa dole aka dakatar da aiki domin a koma wani gefen da za asamu ruwa.
Argungu ya yi kira ga mutane da su rika kula da rijiyoyin da aka giggina saboda jama’a su mori abin, maimakon a sa ido wasu na lalatawa ba a yi la’akari da irin makudan kuɗaɗen da aka kashe a wajen gina waɗannan rijiyoyi ba.
Discussion about this post