Sakamakon gwajin cutar korona da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa mutum 19 suka mutu a Najeriya a sanadiyyar kamuwa da Korona.
Adadin yawan mutanen da cutar ta yi ajalin su a kasar nan yanzu ya kai mutum 2,742.
Hukumar ta kuma sanar cewa a wannan rana mutum 290 suka kamu a jihohi 14 da Abuja.
Zuwa yanzu mutum 207,210 ne suka kamu da cutar a kasar nan. an sallami 194,796 sannan har yanzu akwai mutum 9,629 dake dauke da cutar.
Idan ba a manta ba a ranar Litini mutum 141 ne suka kamu da cutar sannan babu wanda ya rasu a dalilin kamuwa da cutar.
A ranar Talata mutum 344 ne suka kamu sannan mutum 8 sun mutu.
Yaduwar cutar
Legas – 77,015, Abuja-22,371, Rivers-12,268, Kaduna-9,759, Filato-9,479, Oyo-8,702, Edo-6,519, Ogun-5,332, Kano-4,200, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,501, Kwara-3,888, Delta-3,514, Osun-2,818, Enugu-2,675, Nasarawa-2,462, Gombe-2,333, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-1,975, Imo-1,973, Bauchi-1,617, Ekiti-1,742, Benue-1,679, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,074, Bayelsa-1,125, Niger-968, Sokoto-796, Jigawa-587, Yobe-501, Cross-Rivers-587, Kebbi-458, Zamfara-276, da Kogi-5.
Bayan haka wani jami’in yada labarai na sashen yi wa mutane allurar rigakafi na jihar Legas Kolawole Oyenuga ya yi kira ga gwamnonin jihohin kasar nan da su rika raba abinci a wuraren da ake yin allurar rigakafin korona cewa yin haka zai domintaimaka wajen samun yawan mutanen da za su bada kansu domin yin allurar rigakafin korona.
Oyenuga dake aiki a cibiyar lafiya na matakin farko dake Ikorodu ya ce tsoton samun matsaloli bayan yin allurar da matsalolin halin rayuwa na daga cikin matsalolin dake hana mutane fitowa yin allurar rigakafin cutar.
Ya ce sanin cewa akwai abinci a wuraren da ake yin allurar rigakafi zai karfafa gwiwowin mutane wajen bada kansu domin yin allurar rigakafin cutar.
Oyenuga ya yi kira ga gwamnati ta kara himma wajen wayar da kan mutane mahimmancin yin allurar rigakafin Korona.
Ya ce da so samu ne mutanen dake fitowa yin allurar rigakafin su fi kwalaben allurar rigakafin da suke da shi yawa a asibitin su