Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa gwamnati za ta katse layukan sadarwa a wasu kananan hukumomin jihar domin jami’an tsaro su samu damar ragargazar ‘yan bindigan da suka buwayi mutane a jihar.
Da yake tattaunawa a wasu tashoshin rediyo a jihar ranar Talata, El-Rufa’i ya yi kira ga mutanen jihar cewa kowa ya zauna cikin shiri gwamnati za ta katsa layukan sadarwa a jihar.
Ya ce layukan sadarwa da za a katse zai fi shafar kananan hukumomin dake da iyakan ƙasa da jihohin Katsina da Zamfara ne.
“Rundunar sojin Najeriya ta bamu shawarar katse layukan sadarwa a wasu kananan hukumomin dake jihar.
“Mun tattauna da jami’an tsaron dake jihar sannan muna jira su nuna mana wuraren da ya kamata a katse layukan sadarwa.
“Na samu izinin yin haka daga wajen shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sannan da zaran jami”an tsaro sun bayyana inda za a katse layukan sadarwa za mu katse ranar Laraba.
“Muna da labarin cewa ‘yan bindiga sun shigo jihar Kaduna domin su rika yin waya da ‘yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa.
A jihar Kaduna Birnin Gwari, Giwa, Chukun, Igabi, Kajuru da Kachia na cikin kananan hukumomin da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga.
El-Rufa’i ya ce gwamnati za ta aika da jami’an tsaro domin tabbatar cewa mutane sun kiyaye dokar hana cin kasuwanin mako-mako da rufe wasu gidajen siyar da man fetur da gwamnati ta saka a jihar.
Ya yi kira ga mutane da su rika sanar wa jami’an tsaro a duk lokacin da suka ga wani ya siya buredi sama da 20 ko ya kawo wayoyin salula da yawa domin a yi masa caji.
Discussion about this post