An bindige mijin Chike Akunyili har lahira a ranar a Enugu, babban birnin Jihar Anambra.
Chike Akunyili miji ne ga tsohuwar Ministar Harkokin Yaɗa Labarai, kuma tsohuwar Hukumar NAFDAC, marigayiya Dora Akunyili.
An bindige shi jim kaɗan bayan ya shiga Enugu, bayan ya koma daga wani taron tunawa da marigayiyar matar sa ɗin da ya halarta.
Ɗan sa Obumneme Akunyili ya tabbatar wa BBC Pidgin da kisan-gillar da aka yi wa mahaifin na sa.
Sai dai da dama na ɗora alhakin kisan a kan Tsagerun IPOB, waɗanda su ka lashi takobin ba za su bari a gudanar da zaɓen gwamnan Anambra, a ranar 6 Ga Nuwamba ba.
An riƙa watsa hoton gawar Akunyili a cikin wani faifan bidiyo a shafukan zumunta na WhatsApp da Facebook.
Discussion about this post