Fitaccen mai daukan hoto kuma jarumi a farfajiyar Kannywood, Ahmed Fage ya rasu ranar Litinin bayan fama da yayi da rashin Lafiya.
Jarumi Ali Nuhu ya wallafa labarin rasuwar Ahmad Tage a shafinsa na Instagram a ranar Litinini in da ya rubuta,
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah Ya yi wa daya daga cikin masu daukar hoto kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Ahmad Tage rasuwa… sakamakon gajeriyar rashin lafiya da ya yi ta fama da ita. Muna rokon Allah Ya jikan sa da rahama,”
Za a yi jana’izar marigayi Tage a makabartar Sabuwar Abuja dake Karamar hukumar Kumbutso, jihar Kano.
Baya ga barkwanci, marigayi Ahmad Aliyu Tage fitaccen mai daukar hoto ne a masana’antar ta Kannywood wanda aka dade ana damawa da shi.
Tuni jaruman masana’antar maza da mata suka shiga alhini kan rasuwar jarumin tare da yi masa addu’ar Allah ya ji kansa.