Yadda ‘yan bindiga suka kashe jami’an tsaro biyu suka saki fursinoni a jihar Kogi

0

Kakakin ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Rauf Aregbesola, Sola Fasure ya tabbatar da aukuwar wannan hari a wata takatda da ya fidda ranar Litinin.

Fasure ya bayyana cewa maharan sun kai harin gidan gyara hali da ke Kabba a cikin daren Lahadi.

” Akwai sojoji 10 yan sanda da jami’an hukumar gidan gyara hali, wato firzin dake Kabba, kuma sun yi bata kashi matuka da ‘yan bindigan sai dai kuma an rasa jami’ai biyu sannan wasu biyu sun bace.

A karshe ministan ya yi kira ga mazauna kusa da firzin din da su kai karar duk wani da basu yarda da shi ba a wannan unguwa.

Idan ba a manta ba, wasu da ake zaton mayakan ‘yan kungiyar IPOB ne sun balle wata gidan yari inda suka saki sama da mutune 1800 dake daure a firzin din.

Share.

game da Author