MARIGAYI MANTU: Sanata Ibrahim Mantu ya rasu yana da shekaru 74

0

An bayyana rasuwar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Mantu.

Iyalan gidan mamacin sun tabbatar da cewa ya rasu bayan wata rashin lafiya, a wani asibiti na kuɗi a Abuja.

Mantu ya rasu ya na da shekara 74 a duniya. Kuma an sanar da cewa za a yi jana’izar gawar mamacin a Masallacin Juma’a na Rukunin Gidajen ‘Yan Majalisa na Apo, ƙarfe 1 na rana.

An haifi mantu a wani ƙauye da ake kira Chanso da ke ƙarƙashin gundumar Gindiri, ta cikin Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato.

Ya riƙe muƙaman siyasa daban-daban a jam’iyyu daban-daban, inda a cikin 1999 aka zaɓe shi Sanatan Filato ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Cikin 2001 ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Ya rasu a Abuja, kuma za a rufe shi a Abuja. Allah ya gafarta, amin.

Share.

game da Author