KWALARA: Mutum 60 sun kamu a jihar Adamawa

0

Kodinatan, Kwamitin dakile yaduwar cutar Kwalara a jihar Adamawa, Selin La’ori ta bayyana cewa mutum 60 ne suka kamu da cutar a jihar.

Selin ta fadi haka ne a taron masu ruwa da tsaki a hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta jihara garin Yola.

Ta ce an shirya wannan taro domin tsaro hanyoyin da za su fi dacewa wajen dakile yaduwar cutar a jihar.

Selin ta ce zuwa yanzu cutar ta bullo a kananan hukumomin Yola ta Arewa, Yola ta Kudu, Girea, Gombi, Mubi ta Arewa da Guyuk.

Ta kuma ce an sallami mutum 60 din da suka kamu da cutar a jihar.

Selin ta ce an kafa cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar guda uku a jihar.

An bude wadannan wurare a Yola, Gombi da Guyuk sannan hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta ci gaba da daukan matakai domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda Kwalara ta ci gaba da yaduwa a kasar nan.

Cutar ta kashe ɗarruwan jama’a a jihohin Arewa maso Yamma da su ka haɗa da Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi.

Babban laifin gwamnati da ya sa cutar ta ci gaba da yaduwa ne rashin maida hankali wajen tilasta tsaftace muhalli da kulawa da sauran fannonin kiwon lafiya kamar yadda ta ke tayar da hankali, ko ta ke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen yayata batun korona.

Share.

game da Author