Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan ta yanke hukuncin hana jami’an SSS da Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami kamo Sunday Igboho.
Mai Shari’a Ladiran Akintola ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Laraba, bayan ya saurari ƙarar da lauyan Igboho, mai suna Yomi Aliyu (SAN) ya shigar.
Yomi Aliyu dai ya shigar da Daraktan SSS da Ministan Shari’a a cikin ƙarar, duk ya maka su kotu, a madadin wanda ya ke karewa, Sunday Igboho.
Akintola ya ce ya gamsu da dalilan da lauyan Igboho ya shigar, shi ya sa ya yanke hukuncin umarnin kada a damƙo shi.
Mai Shari’a ya hana jami’an tsaro su kashe Igboho ko kamo shi, ko tsare shi ko ci masa mutunci.
Sannan kuma ya hana su takura masa, ko su shiga haƙƙin sa, ko su tauye masa ‘yanci ko hana shi walwala da zirga-zirga, ko hana shi kwana gidan sa, ko kuma kai masa farmaki a gida.
Mai Shari’a ya kuma hana a kulle wa Igboho asusun ajiyar sa na banki, ko ma wane banki ne a faɗin ƙasar nan.
Lauyan ya shaida wa kotu cewa jami’an SSS sun lalata wa Igboho dukiya kuma sun kashe ɗaya daga cikin mazaunin gidan sa, a daren da su ka kai farmaki a gidan Igboho ɗin.
Ya nuna wa kotu irin bayanan irin ɓarnar da ya ce jami’an tsaro sun yi a gidan Igboho, kuma ya miƙa wa kotu adireshin gidan Igboho.