Hukumar dakile yaduwar Kanjamau ta ƙasa NACA ta bayyana cewa waɗanda basu taɓa yin aure ba sun fi kaso mafi yawa cikin waɗanda suke fama da Ƙanjamau a Najeriya.
Akalla kashi 64% daga cikin waɗanda ke dauke da cutar duk marasa aure ne.
Shugaban hukumar Gambo Aliyu ya sanar da haka ranar Litini a Abuja.
Aliyu ya ce mata masu shekaru 17 zuwa 35 da maza mamadu shekaru 19 zuwa 31 ne suka fi kamuwa da cutar.
” Karuwai mata sun fi yaɗa cutar fiye da maza Ƴan luwadi.
Dalilin yin binciken
Aliyu ya ce an gudanar da wannan bincike ne domin gano rukunin mutanen da suka fi yaɗa cutar a kasar nan.
Ya ce gwamnati za ta yi amfani da sakamakon domin tsara ingantattun hanyoyin da suka fi dacewa domin dakile yaduwar cutar.
Daga nan sai Aliyu ya ce gwamnati za ta rika bin mata masu ciki zuwa gidajen su domin wayar musu da kai sanin mahimmancin yin gwajin Kanjamau da karban magani domin kare ƴaƴan su daga kamuwa da cutar a lokacin da suke da ciki.
Ya ce bincike ya nuna cewa mata masu ciki sun kai kashi 22% dake dauke da cutar a Najeriya.
“Domin rage yaduwar cutar ne muka amince mu rika bin mata masu ciki gidajen su domin ba su maganin kare su da ‘ya’yan su daga kamuwa da cutar.
Bayan haka Aliyu ya ce gwamnati za ta rika bin matasa gida-gida domin faɗakar dasu sanin mahimmancin karban magani domin kare kansu daga kamuwa da cutar.