SAMAR DA ABINCI: Bankin CBN ya ce ya bada rancen naira biliyan 791 ga manoma miliyan 3

0

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ya r
aba bashin naira biliyan 791 ga manoma fiye da miliyan 3 da ke cikin jihohin ƙasar nan 36.

Daraktan Harkokin Kuɗaɗe na CBN, Yusuf Yila ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, cikin wata tattaunawa da ya yi da manema Labarai.

Yila ya ce wannan bashi an bayar da shi ne a ƙarƙashin shin bunƙasa noma domin samar da wadataccen abinci a cikin ƙasa na Anchor Borrowers Program, shirin da bankin CBN ke bai wa ƙananan manoma rancen kuɗaɗen noma.

Yila ya ƙara da cewa CBN ya rage kuɗin ruwan lamunin da ya ke bayarwa ga manoman, daga kashi 9 bisa 100 zuwa kashi 5 bisa 100, domin a riƙa ƙara samun manoma da yawa masu buƙatar karɓar lamunin.

An ƙaddamar da shirin bai wa manoma lamunin bunƙasa noma a ranar 17 Ga Nuwamba, 2015, ta yadda za a riƙa ba su lamunin kayan aikin gona da kuma kuɗaɗe ga su Ƙananan Manoma ɗin wato SHF, da a Turance ake kira ‘Small Holder Farmers’.

Shirin dai gwamnati ta ƙirƙiro shi ne domin bunƙasa noman wasu nau’ukan kayan abincin da ta yanka wa ƙa’ida ta ce su ta ke so a riƙa nomawa a ƙasar.

Ana bayar da rancen ne a ƙarƙashin ƙungiyoyin manoma nau’ukan abinci daban-daban.

Lamunin a cewar Yola ya ƙarfafa wa manoma kuzarin samun ƙarin yalwar amfanin gona, ta yadda a baya wanda ke noma masara tan biyu a cikin fili mai faɗin kadada ɗaya, yanzu ya na iya noma masara mai yawan tan biyar a cikin fili mai faɗin kadada biyar.

Yila ya ce albarkacin wannan lamuni a yanzu akan iya noma shinkafa mai yawan tan biyar metrik tan huɗu a cikin kadada ɗaya.

Darakta Yila ya kuma ce CBN na ƙarfafa wa manoma dabarun rage asarar da su ke yi bayan sun girbe amfanin gogar su a lokacin kaka.

Ya ce ta hanyar bunƙasa noman rani su ke yin wannan hikimar. Kuma a cewar sa dabarar ta na rage yawan asarar amfanin gona ƙwarai da gaske.

“Saboda a gaskiya harkokin noma sun fi alfanu a lokacin rani, saboda manomi ba ya iya rage yawan ruwa ko magance ambaliyar ruwa da damina. Amma idan lokacin rani ne, za ka iya amfani da ruwa iyakar yadda ka ke so kuma a lokacin da ka ke so idan noman rani na lambu ka ke yi.

“Sannan kuma CBN ya na gina rumbuna da madatsun ruwa domin rage asarar kayan abinci da ake yi.”

Share.

game da Author