‘Yan Najeriya su daina kula farfaganda da sharrin da ‘Tsagerun Biafra’ ke wa Sojojin Najeriya

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya, ta yi kira ga ‘yan Najeriya ta yi watsi tare da yin kira da a daina kula farfaganda, ƙarya da sharrin da ‘Tsagerun Biafra’ ‘yan ESN ke haɗawa domin ɓata sunan Sojojin Najeriya.

Kakakin Sojoji, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Fitar da wannan sanarwar ya biyo bayan ɓullar wani bidiyo da Nwachukwu ya ce sharri ne da su ka gano cewa ‘yan ESN/Tsagerun Biafra’ ne su ka ƙalla shi.

“Wani bidiyon da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya, wanda ya yi biji-biji bai fito sosai ba, ya nuno wasu mutane sanye da koren kaki, su na lalata sukar da ke cikin wata gona. Kuma su ka ce wai sojojin Najeriya ke yin wannan aika-aikar.

“Da mu ka bi diddigi sai mu ka gano cewa ƙage ne da sharri ‘Tsagerun Biafra’ su ka watsa tun fil-azal a wata tashar su ta ‘Youtube’ mai suna BIAFRA BOY’, su ka ce wai sojojin Najeriya ne.

“Mun gano cewa ba sojojin Najeriya ba ne. Mun gano cewa da gangan aka maida bidiyon biji-biji, don kada a gane ko su wane ne, don kawai a ce sojojin Najeriya ne.

“Sannan kuma ba a bayyana sunan mai gonar da aka lalata wa amfanin gona ba. Ba a faɗi ƙauyen da gonar ta ke ba, ko cikin wace ƙaramar hukuma ko jiha.” Inji mahukuntan Sojojin Najeriya.

Don haka sun ce a yi watsi da irin wannan sharri da soki-burutsu. Kuma kada jama’a su gaji wajen bai wa sojojin Najeriya haɗin kai domin wanzar da tsaro a ƙasar nan.

Share.

game da Author