KOWANE GAUTA JA NE: Babban Basaraken Ibadan ya tura tawagar goyon bayan Sunday Igboho a Kwatano

0

Babban Basaraken ƙasar Badun, Olubadan na Daular Yarabawan Ibadan da kewaye, Saliu Adetunji, ya aika da babbar tawaga zuwa Kwatano, baban birnin ƙasar Jamhuriyar Benin, domin su je kotu su saurari zaman da za a yi kan shari’ar gogarma Sunday Igboho da aka kama a ƙasar.

Kakakin Yaɗa Labarai na Fadar Basarake Olubadan, Adela Oloko ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, cikin wata sanarwa da ya fitar, da yawun basaraken.

Ya ce Olubadan ya yanke shawarar tura tawagar ce bayan da ya yi wata keɓantacciyar ganawa da Majalisar Kare Haƙƙin Gurguzun Yarabawa Haifaffun Ibadan, a fadar sa.

Ya ƙara da cewa kuma ya yi hakan ne domin ya nuna wa masu damun sa da waya da masu zanga-zanga cewa bai fa naɗe hannaye da ƙafafuwan sa ya zura idanu kawai ya ƙyale Sunday Igboho ba.

“Sunday Igboho na mu ne, mazaunin Ibadan ne, ya yi aure a Ibadan, ya raini ‘ya’yan sa a Ibadan, ya gina gidaje a Ibadan. Saboda haka ya na da haƙƙi a kan mu na kare masa ‘yancin sa daidai yadda doka ta tanadar.

Olubadan ya nuna damuwar cewa kada wannan dambarwar da ake yi ta sake haifar da ƙaramin yaƙin da aka taɓa yi tsakanin Yarabawa da Fulani a cikin 1814.

A yau Litinin dai za a gurfanar da Igboho a kotun Kwatano, yayin da a ɗaya ɓangaren kuma Najeriya na matsa-ƙaimin mahukuntan Jamhuriyar Benin su damƙa mata gogarman, domin ya girbi hukuncin abin da ya aikata.

Share.

game da Author